TAMBAYOYI (90) DA AMSOSHINSU GAME DA IMAM HUSAINI (A.S)



     
                                 

                                         GABATARWA
Dukkan yabo ya tabbata ga Ubangiji, tsira da aminci su kara tabbata ga fiyayyen halitta annabi Muhammad tare da iyalansa tsarkaka.
Wannan littafi yana dauke da tambayoyi guga casa’in (90) tare da amsoshinsu game da halifa na uku, wato imam Husaini (a.s), tun daga haihuwarsa har zuwa shahadarsa. An fito da wadannan tambayoyi ne sakamakon musabakar da aka yi wa daliban makarantar Hauzatu Bakiril’ulum (a.s) da ke Dambare ranar Tasu’a ta shekarar 2013 miladiyya a Husainiyyar da ke makarantar.
Mun fito da tambayoyin ne muka mayar da su littafi domin sauran dalibai su amfana da da su. Kuma wadannan tambayoyi da amsoshi an fassara su ne daga littafin KADATUNA. Haka kuma hujjatul Islam walmuslimin  Sheikh Muhammad Nur shi ne ya duba wadannan tambayoyi.

MUJTABA SHU’AIBU ADAMU
Hauzatu Bakiril’ulum, Kano
10 – 10 - 2015
السلام على الحسين وعلى علي ابن الحسين وعلى أولاد الحسين وعلى أصحاب الحسين





TAMBAYA
AMSA
1
A wane wata aka haifi imam Husaini?
A watan Sha’aban.
2
A wace shekara aka haifi imam Husaini?
A shekara ta hudu bayan hijira
3
Wace ce mahaifiyar imam Husaini (a.s)?
Nana Fadimatu (a.s)
4
Shekarun imam Husaini nawa lokacin da ya yi shahada?
Shekarunsa 57.
5
A ina aka haifi imam Husaini (a.s)?
A Madina
6
A ina aka binne shi?
A Karbala
7
Ya ake kiran ranar da imam Husaini ya yi shahada?
Ashura
8
Ya sunan matar imam Husaini wadda ta haifi imam Aliyu Zainul Abidina?
Shazana ‘yar Yazdajir.
9
Nawa ga wata imam ya yi shahada?
10 ga watan Muharram.
10
Su wane ne shugabannin samarin aljanna?
Imam Hasan da Husaini
11
Mece ce alkunyar imam Husaini (a.s)?
Baban Abdullahi
12
A zamanin wane sarki imam Husaini ya yi shahada?
Yazidu dan Mu’awiya.
13
Imamai nawa ne daga ‘ya’yan imam Husaini?
Imamai 9 ne.
14
Hajji nawa imam Husaini ya je da kafarsa?
Hajji 25.
15
Wa imam Husaini ya aika zuwa ga mutanen Kufa?
Muslim dan Akil.
16
Wane ne ya jagoranci rundunar da ta fara tare su imam Husaini?
Hurru dan Yazid Arriyahi
17
Yaya sunan wanda ya fara harbin imam Husaini da sahabbansa?
Umar dan Sa’ad
18
Me Umar dan Sa’ad ya fadi lokacin da ya harbi su Imam Husaini?
Ku shede ni a wajen sarki cewa ni ne na fara harbin Husaini.
19
Sahabban Imam Husaini su nawa ne a filin Karbala?
Su 36 ne.
20
Wane ne ya sari imam Husaini a hannunsa na hagu har ya cire shi?
Zar’atu dan Shuraik Tamimi.
21
Wane ne ya sare kan imam Husaini (a.s)?
Shimru dan Ziljaushan.
22
Wane ne na karshen shahada a sahabban imam Husaini?
Suwai dan abi Muda’i.
23
Wane jagora ne daga rundunar Yazidu ya tuba ya komo cikin rundunar imam Husaini?
Hurru dan Yazid Riyahi.
24
Wane ne ya saura (namiji) daga rundunar imam Husaini ba a kashe shi ba?
Imam Aliyu Zainul Abidina.
25
Karashe fadin Imam Husaini: Ba zan yi muku bai’a da hannuna ba . . . 
Ina kaskantacce 

26
Wane ne ya jagoranci tawayen masu tuba (التوابين)?
Sulaimanu dan Surd.
27
Wane ne ya dauki fansar kisan imam Husaini?
Mukhtar Assakafi.
28
Wane ne sarki a garin Kufa lokacin da aka kashe imam Husaini?
Ubaidullahi dan Ziyad.
29
Ta yaya aka kashe Muslim dan Akilu?
An sare kansa aka jeho shi daga kan hasumiyar fada.
30
Wace rana Muslim dan Akil ya yi shahada?
Ranar 8 ga Zulhijja.
31
Wasiku nawa mutanen Kufa suka aika wa imam Husaini suna nemansa da ya tawo wurinsu su taimake shi?
Wasiku dubu arba’in.
32
Me ya sa imam Husaini ya fita daga Madina?
Don kada a halarta ta da kashe shi.
33
Me aka yi alkawarin za a ba wa Umar dan Sa’ad idan ya kashe imam Husaini?
Za a nada shi sarki a garin Rayyi.
34
Karasa wannan taken: ... كل أرض كربلاء؟
كل يوم عاشوراء ...
45
Wane ne ya biyo su imam Husaini ya yi tarayya da su?
Habibu dan Muzahir
36
Wane ne ya rike tutar imam Husaini?
Abbas dan Ali
37
Me imam Husaini ya ce da Hurru lokacin da ya zo ya tuba?
Kai da ne in Allah ya yarda a Duniya da Lahira.
38
Wane ne ya fara fafatawa daga rundunar imam Husaini?
Abdullahi dan Umair.
39
Me imam Husaini ya tuna ana tsaka da yaki?
Ya tuna Salla a farkon lokacinta.
40
Wane ne ya kashe Habibu dan Muzahir?
Hussaini dan Tanitu.
41
Karasa fadin Aliyul Akbar: Ni ne Aliyu dan Husaini …
Na rantse da ubangijin Ka’aba mu ne muka fi cancanta da annabi, wallahi dan dan karuwa ba zai mulke mu ba.
42
Me ya sa ake kiran Ubaidullahi dan Ziyad da dan dan karuwa? Ko dan Kire?
Saboda shi Ziyad dan karuwa ne, sai abu Sufyan ya karbe shi ya danganta shi ga kansa.
43
Wane jariri ne daga ‘ya’yan imam Husaini aka harbe shi da kibiya yana hannu babansa?
Abdullahi dan Husaini.
44
Fadi ‘yan uwan imam Husaini biyu da aka kashe su tare da imam din.
Abdullahi dan Ali da Ja’afar dan Ali.
45
Karasa fadin imam Husaini (a.s) ga wadanda suke yakarsu: “Idan ba ku da addini …
…ku zama ‘ya’ya a rayuwarku ta duniya”.
46
Wane ne ya harbi imam da kibiya?
Sinan dan Anas Nakha’i.
47
Wane ne ya binne imam Husaini da sahabbansa?
Mutanen bani Asad tare da Zainul Abdina.
48
Mutum nawa aka kashe daga ‘yan uwan imam Husaini ta bangaren mahaifinsa?
Mutum shida.
49
Wane ne ya kashe Abbas dan imam Ali?
Zaidu dan Dauda da Hakim dan Dufail.
50
A wace shekara aka yi tawayen Tawwabin?
Shekara ta 65 bayan hijira.
51
Su wane ne ‘yan Tawwabin?
Wadanda suka tozarta imam Husaini kuma suka yi nadama da hakan.
52
Wane ne ya kashe Umar dan Sa’ad?
Mukhtar Assakafi?
53
Me ake nufi da: (قل تعالو ندع أبناءنا) a Alkur’ani?
Su ne: Hasan da Husaini.
54
Karasa fadin imam Husaini (a.s): “Na fito ne don neman…
…gyara  a cikin al’ummar kakana”.
55
Karasa fadin imam Husaini (a.s): “Ba na ganin mutuwa face rabauta …
…rayuwa (kuwa) da azzalumai illa tabewa.
56
Wane ne mafi kankata daga ‘ya’yan imam ya yi shahada tare da imam Husaini (a.s)?
Alkasim dan Husaini.
57
Su wane ne Ashabul kisa’i?
Manzon Allah da Fadima da Ali da Hasan da Husaini (a.s)?
58
Me ya faru da damkin kasar Karbala wadda manzon Allah ya ba wa Ummu Salama?
Ta zama jini lokacin da aka kashe imam Husaini.
59
Shekara nawa imam ya rayu tare da kakansa manzon Allah?
Kasa da shekaru bakwai.
60
Karasa fadin manzon Allah ga imam Husaini: “Ya Allah ina sonsa …
…ka so shi, ka so wanda yake sonsa”.
61
Sau nawa imam Husaini ya yi hajji a kasa?
Sau 25.
62
A gidan wa Muslim dan Akil ya sauka a garin Kufa?
A gidan Mukhtar Assakafi.
63
Wane ne mutanen Kufa suka tarbe shi da sunan shi ne imam Husaini (a.s)?
Ubaidullahi dan Ziyad.
64
Wane ne wanda imam Husaini ya ce: “An karya bayana” lokacin da aka kashe shi?
Dan uwansa Abbas dan imam Ali.
65
Karasa fadin mawaki: Yanzu al’ummar da ta kashe Husaini za ta so …
…ceton kakansa ranar hisabi?
66
Wurare nawa ake cewa an binne kan imam Husaini a wurin?
Wurare tara ne.
67
Shekarun Abbas nawa lokacin da ya yi shahada?
Shekaru 34.
68
‘Yan uwan Muslim dan Akil nawa ne suka yi shahada tare da imam Husaini (as.)?
Su uku ne: Abdullahi da Ja’afar da Abdurrahman.
69
Wane ne daga Banu Hashim ya fara yin shahada a Karbala?
Ali Akbar dan imam Husaini.
70
Me imam Rida ya yi umarni a rinka cewa idan an tuna bala’in Karbala?
“Ina ma mun kasance tare da ku, da mun rabauta da babban rabo”.
71
Habibu dan Muzahir yana daga cikin sahabban annabi?
Yana cikinsu.
72
Shugaban wace kabila ne Habubu dan Muzahir?
Kabilar Asad.
73
Wane ne mafi kankantar shekaru a sahabban imam Husaini?
Amru dan Jinadata mutumin Madina.
74
Wane ne daga cikin jikokin imam Husaini ya jagoranci tawaye ga Umayyawa?
Zaidu da Ali da Husaini.
75
Imamai nawa ne suke da suna Husaini?
Mutum daya ne.
76
Wadanne abubuwa ne suka fi soyuwa ga Yazidu?
Shan giya da farauta da kare.
77
Nawa ne adadin rundunar Umar dan Sa’ad?
Fiye da 4000
78
Me imam Husaini ya nema daga mutanensa da daddare kafin a fara yaki?
Ya nemi su sulale cikin dare.
79
Ya sunan matar da ta boye Muslim dan Akin a gidanta?
Sunanta Dau’a.
80
Me ‘ya’yan Muslim suka fada lokacin da suka sami labarin kashe mahaifinsu?
Sun ce: “Wallahi ba za mu huta ba har sai mun dauki fansa ko kuma mu ma mu dandani abin da ya dandana.
81
Wa imam Husaini ya aika ya debo musu ruwa?
Dan uwansa Abbas dan imam Ali.
82
Fadi mutum biyu daga sahabban imamu Husaini da suka yi shahada tare da shi.
Muslim dan Ausaja da Zuhairu dan Kain.
83
Wane ne daga sahabban imam Husaini ya ce: “Tsakaninmu da ‘Hurul’ini’ (matan aljanna) kawai wadancan su auko mana”?
Barbar dan Hudair Hamdani.
84
Wane ne farkon wanda ya yi shahada daga sahabban imam Husaini (a.s)?
Muslim dan Ausaja.
85
Wane ne ya harbi imam Husaini da kibiya a bakinsa?
Hussaini dan Tanimu.
86
Wace mace ce ta yi Khuduba a Kufa bayan Zainab?
Fadimatu ‘yar imam Husaini.
87
Shekaru nawa imam Husaini ya rayu tare da mahaifinsa imam Ali (a.s)?
Fiye da shekaru 30.
88
Wace aya imam  Husaini ya rinka karanta ta yayin fitarsa daga garin Makka?
(رب نجني من القوم الظالمين)
Allah ka tseratar da ni daga azzaluman al’umma.
89
A wane gari aka binne imam Husaini (a.s)?
A Karbala.
90
Wane imami ne bayan imam Husaini (a.s)?
Imam Aliyu Zainil Abidina.


Comments