TSARABAR YARA
DAGA
AHLULBAITI (A.S)
NA
MUJTABA
SHU’AIBU ADAMU
mujtabakano@yahoo.com
2009
GABATARWA SHEIKH NUR
Da
sunan Allah mai rahama mai jin kai. Tsira
da amincin Allah su tabbata ga
manzon Allah da iyalan gidansa tsarkaka.
Wannan
littafin da ke hannunka, an yi bayanin abubuwa ne a saukake, wanda wadannan
abubuwan suna da muhimmanci ga dalibi ya san su. To kasantuwar marubucin ya yi
gogayya da koyarwa na tsawon lokaci, wanda hakan ya ba shi damar sanin halin da
yara dalibai suke ciki na bukatuwa ga akidu da za a saukaka musu fahimtarsu,
don haka wannan marubucin namu ya yi hobbasa domin taimakawa a wannan fage.
Muna
fata Allah ya kara masa basira, kuma Allah ya sa ya zama guzuri a gare shi gobe
kiyama.
Sheikh Muhammad Nur.
Shugaban Mu’assasar Rasulul
A’azam (S.A.W)
GABATARWAR MAWALLAFI
Dukkan yabo ya tabbata ga
Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga annabi Muhammadu
tare da iyalansa tsarkaka.
Wannan littafi ya kunshi bayanan
abubuwa uku: Ginshikan Musulunci da rassanssa da kuma Tarihi. Wanda aka rubuta
shi da sassaukan salo domin saukaka wa yara fahimtar Akidar Musulunci
ingantacciya, wadda ta zo daga Ubangijinmu ta hanyar annabinsa Muhammad (S.A.W),
kana ta biyo ta kan Ahlulbait wato iyalan gidansa tsarkaka, wadanda Allah ya
tafi da dukkan datti daga gare su, ya tsarkake su tsarkakewa.
A karshe
ina mai godiya tare da jinjina ga malamaina, musamman Sheikh Muhd Nur Shugaban
Mu’assasar Rasulul A'azam (S.A.W) da Sheikh Bashir Lawal da Sheikh Saleh Muhd
Sani da dukkanin ma'aikatanta da ‘yan uwana dalibai da ‘yan majamu’a baki daya.
Allah ya sa mu dace.
Mujtaba
Shu'aibu Adamu
Hauzatu
Bakirul Ulum Kano
KASHI NA FARKO
AKIDAR
MUSULUNCI
Yana da
kyau yaranmu su haddace wadannan jumloli masu zuwa:
1.
Allah
ne Ubangijinmu.
2.
Muhammadu
ne annabinmu.
3.
Musulunci
ne addininmu.
4.
Ka'aba
ce alkiblarmu.
5.
Alkur'ani
ne littafinmu.
6.
Dukkan
Musulmi 'yan uwanmu ne.
1 – ALLAH NE UBANGIJINMU:
Kamar yadda muka san cewa gine-ginen da muke ciki
ko kuma muke gani, da motocin da muke shiga ko kuma muke gani masu kyawun gani,
haka nan suturun da muke sakawa masu kyawun launi ba su ne suka yi kansu ba,
mun san cewa akwai wani kwararre da ya kera su da wannan kyawun da muke iya
gani. To ita ma sama da muke gani mai fadin gaske, tare da rana da wata da taurari.
Ga kuma kasa mai fadi da muke zaune kuma muke yawo a kanta, lallai akwai wanda
ya halicce su da wannan yanayin da muke ganinsu.
To haka nan muma mutane da muke raye, muke
numfashi, muke gani da idanu biyu, muke da hannaye biyu da kafafuwa biyu,
lallai akwai wanda ya halicce mu.
To wane ne ya halicce mu?
Wannan da ya halicci sammai da kassai da rana da
wata da koramu da dabbobi, shi ne ya halicce mu, wato ALLAH, shi
ne Ubangijinmu kuma shi ne mai iko a kan
komai, shi ne kuma ya halicci kowane abu domin ya yi hidima ga mutum, lallai
Ubangijinmu ya girmama mu!
Ya cancanci mu gode masa, kuma mu bauta masa bisa
cancanta domin wannan ni'ima da ya yi mana.
2 – MUHAMMADU NE ANNABINMU:
Kamar yadda kowane yaro yake bukatar uwa da uba,
ko bukatar dalibi ga malamai, haka nan mutum yake bukatuwa ga annabi wanda zai
shiryar da shi hanyar alkhairi, ya kuma hana shi bin hanyar da zai halaka.
Allah madaukakin sarki ya aiko annabwa da dama, sai ya sanya mu a cikin
al'ummar Annabi Muhammadu (S.A.W).
Annabawa Iri Biyu Ne:
·
Akwai annabawan da Allah ya aiko su zuwa
ga mutanen wani gari ko kauye. Kamar su:
Annabi
Hudu da Annabi Salihu da Annabi Yunus da Annabi Shu'aibu da Annabi Zakariyya da
makamantansu.
·
Akwai kuma Annabawan da Allah ya aiko su
domin su shiryar da dukkan mutanen duniya. Kamar su:
Annabi Nuhu (A.S) da Annabi Ibrahim (A.S) da
Annabi Musa (A.S) da Annabi Isa (A.S) da kuma Annabi Muhammadu (S.A.W) annabin karshe,
wanda babu wani annabi a bayansa, kuma shi ne annabin da Allah ya aiko mana, mu
mutanen karshe har zuwa tashin Alkiyama.
3 – MUSULUNCI NE ADDININMU:
Sunan addinin annabi Muhammadu MUSULUNCI,
don haka mu musulmi ne masu biyayya ga Muhammad annabin Allah (S.A.W), domin
bin sa bin Allah ne, saba masa kuma saba wa Allah ne, shi ne wakilin Allah a
tare da mu. Haka kuma muna yin biyayya ga iyalan gidansa domin su ne wakilansa
a tare da mu, wadanda ya yi mana wasici da su, a bisa fadinsa cewa: Na bar muku
abubuwan da idan kuka yi riko da su a bayana ba za ku bata ba: Littafin Allah
da iyalan gidana.
MECE CE KALMAR
SHAHADA:
(أشهد
أن لاإله إلا الله, وأشهد أن محمدا رسول الله).
MA'ANA:
NA SHAIDA BABU ABIN BAUTAWA DA GASKIYA SAI ALLAH,
KUMA ANNABI MUHAMMADU MANZONSA
NE.
Duk wanda
ya furta wannan kalma yana mai imani da ita ya zama Musulmi, jininsa da
dukiyarsa da mutuncinsa ya haramta a taba masa, sakamakonsa yana ga Allah.
Kamar yadda ya zo a hadisi ingantacce daga manzon Allah (S.A.W).
4 – KA'ABA CE ALKIBLARMU:
Dukkanin Musulmi dakin Allah mai alfarma na
Ka'aba suke fuskanta su yi salla, na kusa da na nesa da ita, salla ba ta inganta
sai da fuskantar alkibla. Har yau a dakin ne Allah ya wajabta a yi aikin Hajji,
ba ya halatta a yi aikin a wani wuri daban.
5 - ALKUR'ANI NE
LITTAFINMU:
Hakika Allah madaukakin sarki ya saukar da
litattafai ga wasu daga cikin annabawansa, domin ya zama shiriya ga al'ummarsu.
Kamar: ATTAURA da INJILA. Littafin da aka saukar wa
annabinmu Muhammadu (S.A.W) shi ne ALKUR'ANI mai girma, littafin
shiriya ga wannan al'umma tun zamanin Annabi har ya zuwa tashin Alkiyama.
6 – DUKKAN MUSULMI 'YAN UWANMU NE:
(أشهد
أن لاإله إلا الله, وأشهد أن محمدا رسول الله).
Na shaida cewa: BABU ABIN BAUTAWA DA
GASKIYA SAI ALLAH, KUMA ANNABI MUHAMMADU MANZONSA NE . Wannan kalma ta hade dukkan Musulmi sun zama daya
a wurin Allah, babu wanda ya fi wani a wurinsa, sai wanda ya fi jin tsoronsa.
Allah ya haramta zubar da jinin Musulmi ko cin
mutumcinsa ko zaginsa. Ya kuma yi alkawarin sakayya ga duk wanda aka zalunta, a
nan duniya ko a lahira.
GINSHIKAN MUSULUNCI
·
Ginshikan Musulunci guda nawa ne?
Ginshikan
Musulunci guda biyar ne.
1. Tauhidi.
2. Adalcin
Ubangiji.
3. Annabta.
4. Imama.
5. Tashin
Alkiyama.
·
Mene ne Tauhidi?
Shaidawa
babu abin bautawa da gaskiya sai Allah.
·
Mene ne Adalcin Ubangiji?
Shaidawa Allah maddukakin sarki mai adalci ne, ba ya
zalunci.
· Mece ce Annabta?
Shaidawa Allah madaukakin sarki ya aiko
annabawa, domin su shiryar da mutane zuwa ga alKhairi, na karshensu shi ne
Annabi Muhammadu (S.A.W).
·
Mece ce Imama?
Shaidawa manzon Allah ya yi wasici da imamai sha biyu a bayansa:
1. Imamu Aliyyu.
2. Imamu Hasan.
3. Imamu Husaini.
4. Imamu Aliyyu
Zainul Abidina.
5. Imamu Muhammadul
Bakir.
6. Imamu Ja’afar
Assadik.
7. Imamu Musa
Al-Kazim.
8. Imamu Aliyyu
Rida.
9. Imamu Muhammad
Al-jawad.
10. Imamu Aliyyu
Al-Hadi.
11. Imamu Hasan
Al-Askari.
12. Imamu Muhammad
Al-Mahdi. (Wanda muke sauraro).
·
Mece ce tashin Al-Kiyama?
Shaidawa Allah madaukakin sarki
zai tashi mutane bayan mutuwarsu, domin ya yi musu hisabi a bisa abin da suka
aikata a gidan duniya, na alkhairi ko na sharri.
KASHI NA BIYU
RASSAN ADDININ MUSULUNCI
·
Rassan addinin Musulunci guda nawa ne?
Rassan
Addinin Musulunci guda goma ne.
1. Salla. 2. Azumi. 3.Zakka.
4. Hajji. 5. Humusi 6. Umarni da kyakkyawan aiki. 7. Hani da mummunan aiki.
8. Jihadi saboda
Allah. 9. Tawalli.
10. Tabarri.
·
Mece ce Salla?
Salla
ibada ce da Allah ya wajabta wa musulmi sau biyar a rana. Su ne:
Ø Azahar Ø La’asar
Ø Magariba Ø Isha’i
Ø Asuba
Sallar Azahar raka’a nawa ce?
Raka’a
hudu ce.
v
Tahiya nawa? Tahiya
biyu.
v
Sallama nawa? Sallama
daya.
v
Karatunta a sarari ake yi ko a boye? A boye.
v
Sallar La’asar raka’a nawa ce?
Raka’a
hudu ce.
v
Tahiya nawa? Tahiya
biyu.
v
Sallama nawa? Sallama
daya.
v
Karatunta a sarari ake yi ko a boye? A boye.
v
Sallar Magariba raka’a nawa ce?
Raka’a
uku ce.
v
Tahiya nawa? Tahiya
biyu.
v
Sallama nawa? Sallama
daya.
v
Karatunta a sarari ake yi ko a boye? Biyun farko a
sarari, dayan karshe a boye
v
Sallar Isha’i raka’a nawa ce?
Raka’a
hudu ce.
v
Tahiya nawa? Tahiya
biyu.
v
Sallama nawa? Sallama
daya.
v
Karatunta a sarari ake yi ko a boye? Biyun farko a
sarari, biyun karshe a boye.
v
Sallar Asuba raka’a nawa ce?
Raka’a
biyu ce.
v
Tahiya nawa? Tahiya
daya.
v
Sallama nawa? Sallama
daya.
v
Karatunta a sarari ake yi ko a boye? A sarari.
Salla ba ta yiwuwa sai da alwala,
saboda fadin Allah madaukakin sarki:
﴿ياأيها الذين آمنوا إذا قمتم إلى الصلواة فاغسلوا وجوهكم وأيديكم
إلى المرافق ومسحوا برؤوسكم وأرجلكم إلى الكعبين﴾.
YA
KU WADANDA KUKA YI IMANI, IDAN KUN ZO YIN SALLA, KU WANKE FUSKOKINKU DA
HANNAYENKU, KU SHAFI KAWUNANKU DA KAFAFUWANKU.
Wajiban alwala guda nawa ne?
Wajiban
alwala guda hudu ne.
- Wanke fuska.
- Wanke hannaye ya zuwa dantse.
- Shafar kai.
4. Shafar kafafuwa[1].
NAJASA
Alwala
ba ta yiwuwa sai an tsarkaka daga najasa. Akwai wasu abubuwan najasa da ya
wajaba mu nisance su, kuma mu tsarkake jikkunanmu da tufafinmu da kayayyakinmu
daga gare su.
Daga cikin su akwai: Fitsari da gayidi da kare da jini da
makamantansu.
Idan najasa mai danshi ta taba jikin mutum ko tufafinsa,
ya wajaba a gare shi ya wanke su da ruwa mai tsarki.
MISALIN YADDA AKE YIN SALLAR
ASUBA
RAKA'A
TA FARKO:



بِسْمِ
اللهِ الرَّحْمنِ الرَّحِيمِِ {1} الْحَمْدُ للّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ {2} الرَّحْمـنِ
الرَّحِيمِ {3} مَالِكِ يَوْمِ الدِّينِ {4} إِيَّاكَ نَعْبُدُ وإِيَّاكَ نَسْتَعِينُ
{5} اهدِنَا الصِّرَاطَ المُستَقِيمَ {6} صِرَاطَ الَّذِينَ أَنعَمتَ عَلَيهِمْ غَيرِ
المَغضُوبِ عَلَيهِمْ وَلاَ الضَّالِّينَ {7}
Sannan
ya karanta cikakkiyar sura, kamar:
بِسْمِ
اللهِ الرَّحْمنِ الرَّحِيمِ{1} إِنَّا أَعْطَيْنَاكَ الْكَوْثَرَ
{2} فَصَلِّ لِرَبِّكَ وَانْحَرْ {3} إِنَّ شَانِئَكَ هُوَ الْأَبْتَرُ {4}

(سُبْحَانَ رَبِّيَ
العَظِيمِ وَبِحَمْدِهِ).
SUBHANA RABBIYAL AZIMI WABIHAMDIHI.
Ko (سُبْحَانَ اللهِ)
SUBHANALLAHI. Sau
uku.

(سَمِعَ اللهُ لِمَن حَمِدَه).
SAMI'ALLAHU
LIMAN HAMIDAH.

(سُبْحَانَ رَبِّيَ الأَعْلَى وَبِحَمْدِهِ).
SUBHANA
RABBIYAL A'LA WABIHAMDIHI.
Ko
(سُبْحَانَ اللهِ) SUBHANALLAHI. Sau
uku.


(سُبْحَانَ رَبِّيَ الأَعْلَى وَبِحَمْدِهِ).
SUBHANA
RABBIYAL A'LA WABIHAMDIHI.

Idan
ya aikata haka, to ya yi raka'a guda cikakkiya, sai ya mike tsaye ya sake
aikata kamar yadda ya yi a raka'a ta farko.
Mustahabbi
ne ya karanta 'Alkunuti' bayan kare karatun sura ta biyu kafin ya yi ruku'u.

اَشْهَدُ أَنْ لاَ إِلَهَ
إِلاَّ اللهُ, وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ.
وَأَشْهَدُ أَنَّ مُحَمَّداً
عَبْدُهُ وَرَسُولُهُ,
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى
مُحَمَّدٍ وَآلِ مُحَمَّد.
ASHHADU
ALLA'ILAHA ILLALLAHU, WAHDAHU LA SHARIKA LAH,
WA
ASHHADU ANNA MUHAMMADAN ABDUHU WA RASULUHU,
ALLAHUMMA
SALLI ALA MUHAMMADIN WA AALI MUHAMMAD.
Sannan
ya yi sallama idan sallar mai raka'a biyu ce. Ya ce:
السَّلاَمُ عَلَيكَ أَيُّهَا
النَّبِيُّ وَرَحْمَةُ اللهِ وَبَرَكَاتُهُ.
السَّلاَمُ عَلَيْنَا
وَعَلَى عِبَادِ اللهِ الصَّالِحِينَ.
السَّلاَمُ عَلَيكُمْ
وَرَحْمَةُ اللهِ وَبَرَكَاتُهُ.
ASSALAMU
ALAIKA AYYUHAN NABIYU WA RAHMATULLAHI WA BARAKATUHU.
ASSALAMU
ALAINA WA ALA
IBADILLAHIS SALIHIN.
ASSALAMU
ALAIKUM WA RAHMATULLAHI WA BARAKATUH.
Idan
kuwa salla mai raka'a uku ce ko hudu, to ba zai karanta sallamar ba, sai a
raka'a ta karshe1.
·
Mene ne Azumi?
Azumi ibada ne da
Allah ya wajabta wa musulmi, kamewa daga barin abin ci da na sha a kwanakin
watan Ramalana, daga fitowar alfijir zuwa faduwar rana ta shari'a.
·
Mece ce zakka?
Ita ce musulmi ya bayar
da wani kaso kididdigagge, daga cikin dukiyarsa, ga talakawa da miskinai.
·
Mene ne Humusi?
Humusi shi ne,
musulmi mukallafi ya bayar (1/5) daga cikin ribar da ya
samu, a karshen kowace shekara.
·
Mene ne Hajji?
Hajji ibada ne da
Allah ya wajabta wa musulmi mukallafi, sau daya a rayuwarsa, ga wanda ya sami
iko.
·
Mene ne Umarni da kyakkyawan aiki?
Shi ne musulmi ya umarci mutane,
ga aikata ayyukan alkhairi.
·
Mene ne Hani da mummunan aiki?
Shi ne musulmi ya hana mutane, ga barin abin da
Allah ya haramta.
·
Mene ne Jihadi?
Shi ne musulmi ya yaki zalunci da dukkan karfinsa.
·
Mene ne Tawalli?
Tawalli shi ne: Son
masoya Allah.
·
Mene Tabarri?
Tabarri shi ne: Kin
makiya Allah.
KASHI NA UKU
SIRAR SHUGABANMU ANNABI
MUHAMMADU (S.A.W)
Shi ne Muhammadu, dan Abdullahi, dan Abdul Mudallabi.
Sunan mahaifiyarsa Aminatu 'yar Wahabi, sunan wanda ya raine shi Abu Dalibi,
sunan wadda ta shayar da shi Halimatus Sa'adiyya, sunan danginsa Banu Hashimu.
MUTUWAR MAHAIFINSA
Mahaifinsa
ya tafi fatauci ya zuwa Sham, a yayin dawowarsa, sai mutuwa ta riske shi a
birnin Madina, sai aka binne shi a can, a sannan matarsa Aminatu tana da cikin
Muhammadu wata biyu. A wannan ranar samarin Makka da manyan Larabawa, da yara
da mataye da tsofaffi sun yi bakin cikin rabuwa da shi, tun ba matarsa ba
Aminatu, da dan uwar haihuwarsa Abu Dalibi da mahaifinsa Abdul Mudallabi, sun
hakura da abin da Allah ya kaddara musu, domin duk wanda Allah ya yi kiransa
tilas ne ya tafi, rahamar Allah ta tabbata ga Abdulahi mahaifin manzon Allah.
HAIHUWARSA DA TARBIYYARSA
Yayin
da shugabarmu Aminatu ta shiga cikin wata na tara
da cikin manzon Allah, wani abu da yake samun mata kamar radadi da ciwon ciki
bai same ta ba, ko wata kazanta ta wurin nakuda.
An
haifi annabi Muhammadu a Makka abar girmamawa. Hakika kakansa Abdul Mudallabi
ya yi matukar farin ciki da haihuwarsa, sai ya ambace shi da Muhammadu. A bisa
al'adar Larabawa a kan
bayar da lada a shayar da 'ya'yayensu a kauye, domin su tashi da fasahar
Larabawa da rayuwar sahara mai tsanani.
A wannan lokacin Halimatu Sa'adiyya ta zo daga kauye ta
nemi a ba ta Muhammadu domin ta shayar da shi. Ta kasance talaka, ba ta mallaki
komai ba sai wasu 'yan tumaki kadan ramammu, sai aka ba ta Muhammadu ta tafi da
shi.
Hakika albarkar Muhammadu ta lullube su lokacin da ta
tafi da shi, sun ga alkhairi mai yawa da albarkatu, arziki ya lullube su,
dabbobinsu suka yi nama da nono, suka yi farin ciki da Muhammadu abin shayarwa.
Muhammadu
ya rayu a gidan Halimatus Sa'adiya tare da 'ya'yanta, sun so shi so mai
tsanani, ya kasance kyakkyawa, mai hankali da ladabi. Yayin da ya kai shekara
shida, sai ta zo da shi wurin kakansa da mahaifiyarsa Aminatu da shi. Suka gan
shi ya zama saurayi, mai tsafta, abin so, suka yi farin ciki da shi. Sai aka ba
wa Halimatus Sa'adiyya ladanta na shayar da Muhammadu tare da kyautatawa.
Tsiran Allah da amincin Allah su kara tabbata a gare shi da iyalan gidansa.
MUTUWAR MAHAIFIYARSA AMINATU
Yayin
da aka dawo da Muhammadu yana karami ya zuwa mahaifiyarsa, sai ta tafi da shi
Yasriba (Madina), domin ziyartar 'yan uwanta kuma ta nuna musu Muhammadu. A
tare da ita akwai mai yi mata hidima, wadda ake kira Ummu Aimana mutuniyar
Habasha.
Lokacin
da suka isa Yasriba, sai dangin mahaifiyarsa Aminatu suka tare su da farin ciki
da annashuwa, suka zauna tsawon wata uku a birnin Madina.
A
yayin dawowarsu zuwa Makka, sai mutuwa ta riski Amina bayan rashin lafiya, sai
aka binne ta a can. Rahamar Allah da gafararsa su tabbata ga Aminatu. Sai Ummu
Aimana ta tafi da shi ya zuwa kakansa Abdul Mudallabi, sai ya karbe shi ya ci
gaba da tarbiyyarsa tare da ba shi kulawa. Ya kasance yana son Muhammadu so mai
tsanani, ba ya rabuwa da shi.
Yayin
da Muhammadu ya cika shekara takwas sai Abdul Mudallabi ya rasu, sai Abu Dalib
ya ci gaba da rainonsa, ya kasance yana son Muhammadu sama da dukkan 'ya'yansa,
ya raine shi tare da dukkan 'ya'yansa, har ya girma ya zama saurayi, sallallahu
alaihi wa alihi wasallama.
AUREN ANNABI DA SAYYIDA KHADIJA
Yayin
da annabi Muhammadu ya cika shekara ashirin da biyar, ya shahara da gaskiya da rikon
amana, sai ya tafi fatauci ya zuwa kasar Sham da dukiyar nana Khadija tare da
mai yi mata hidima, wanda ake kira Maisara.
Yayin
da Muhammadu ya dawo daga Sham, sai Khadija ta ga albarka mai yawa tare da rikon
amana a tare da shi, irin wanda ba ta taba gani a wurin wanin Muhammadu ba
(S.A.W). Sai ta aika masa da ya aure ta, sai ya aure ta. Ta kasance mace mai ladabi da biyayya ga annabi
Muhammadu (S.A.W), ta sadaukar da dukiyarta wajen taimakon Addinin Musulunci.
TARIHIN IMAMU ALIYU (A.S)
Wane
ne Imamu Aliyu?
Imamu
Aliyu shi ne dan uwan Annnabi Muhammadu, wanda suke 'yan maza zur, kuma mijin
shugabar matan duniya da Aljanna, nana Fadimatu 'yar annabi Muhammadu (S.A.W).
Sunan
mahaifinsa Abu Dalibi, sunan wadda ta haife shi Fadimatu 'yar Asad.
HAIHUWARSA DA TARBIYYARSA
An
haifi Imamu Aliyu ranar juma'a, uku (3) ga watan Rajab a cikin dakin Allah mai
alfarma (a Ka'aba), kafin a aiko manzo da shekara goma sha biyu (12).
Lokacin
da Fadimatu ta ji ciwon nakuda, sai ta shiga cikin Ka'aba mai alfarma, ta daga
hannayenta ya zuwa sama, tana cewa: Ya Ubangiji na yi imani da kai da kuma
dukkanin litattafan da ka saukar (ga manzanninka), na kuma gasgata kakana
Annabi Ibrahim badadinka (A.S) shi ne ya gina (wannan) daki mai daraja. (Ya
Allah na roke ka) domin wanda ya gina wannan daki da kuma abin da ke cikina ka
saukaka mini wahalar haihuwa[2].
Ba ta kara ko sa'a guda ba ta haihu lafiya sumul kalau.
Yayin da imamu Aliyu ya cika shekaru hudu, sai annabi
Muhammadu ya karbe shi, ya ci gaba da tarbiyyarsa na daga abin da Ubangiji ya
sanar da shi, bai taba rabuwa da shi ba har ya koma ga mahaliccinsa.
Imam
Aliyu ya yi imani da annabi Muhammadu bayan nana Khadija, wani abu na jahiliyya
bai shafe shi ba.
GWARZONTAKAR IMAMU ALIYU
Imam
Aliyu ya kasance wazirin annabi Muhammadu tun yana karami, ya bayar da dukkan karfinsa
wajen taimakon manzon Allah, ya kasance yana biye da shi a duk inda yake, yana
tare masa cutarwar yaran kuraishawa gwargwadon iko.
Bayan
shekaru sha uku (13) da aiko Anabi Muhammadu, kafiran kuraishawa suka kulla makircin
kashe Annabi, sai Allah ya umarce shi da yin hijira daga Makka zuwa Madina.
Imam Ali ya bayar da rayuwarsa fansa ga Muhammadu (S.A.W), inda ya kwanta a
shinfidar manzon Allah har annabi ya kubuta daga sharrin mushirikai.
JIHADINSA A MADINA
Imam
Aliyu ya halarci dukkanin yake-yaken da aka yi da kafirai a zamanin manzon
Allah, banda yakin Tabuka a bisa umarnin manzon Allah (S.A.W). Haka kuma ya
bayar da gudummawa mai yawa a dukkanin yakokin.
Daga
cikin yakokin da ya halarta, akwai: Yakin Tabuka da Uhdu, da Yakin Khandaku da
Khaibara da bude Makka. Allah ya kara yarda a gare shi.
IMAMU ALIYU BAYAN WAFATIN
MANZON ALLAH
Hakika
halifancin Muhammadu (S.A.W) hakkin Imamu Aliyu ne, saboda fadin manzon Allah:
"Wanda na kasance shugabansa, Aliyu ma shugabansa ne". Sai dai yanayi
bai ba shi damar karbar ragamar shugabancin a hannunsa ba, sai ya yi tarayya da
sauran Musulmi wajen neman hadin kai don karfafa Musulunci.
Ya
karbi shugabanci bayan kashe Usmanu dan Affana, ya yi mulki na shekara biyar
(5), ya yi shahada a hannun Abdurrahmanu dan Muljamu (la'anar Allah ta tabbata
a gare shi) a masallaci, aka binne shi a garin Najaf.
MANAZARTA
*
Assaiyid Hashim Musawi: Attarbiyyatul
Islamiyya (na daya).
*
Al’Islam Risalatuna Na Jam’iyyatu
Ta’alimuddin Al’islami.
*
Nafahatun Minassira Na Mu’assasar Albalagh.
*
Kabasatun Minassira Na Munazzamatul
Alamiyya Lilhauzat Walmadarisil Islamiyya
WARARE
DA ZA A SAMI WANNAN
LITTAFIN
1
– Hauzatu Bakirul Ulum (A.S) da ke Dambare Kano, a wurin: Abdullahi Muhammad
Musa 07035858839.
2
– Rasulul A’azam bookshop Tal’udu kusa da Dagedage supuer market Kano, a wajen: Nasiru
Yusuf 08066667564.
3
– Rahama bookshop kwanar taya titin kofar Dawanau daidai kwanar kutare Kano, a wurin: Malam
Garbati 08066075031.
[1] Lallai ne xalibai su sani
cewa: Alwala ba ta yiwuwa sai da Niyya, hakanan dukkanin sauran ibadu. Sai an
qudurce cewa za a yi alwalar ne domin neman yardar Allah ta'ala. Haka kuma
alwala tana da sunnoni kamar:
·
Wanke hannaye zuwa 'ku'u'
(wuyan hannu), sau xaya ko kuma sau uku.
·
Kuskurar baki, sau xaya ko sau uku.
·
Shaqa ruwa, sau xaya ko kuma sau uku.
1 Sai
ya tashi ya kawo raka'a xaya sannan ya yi ruku'u (ko kuma ya karanta wannan
tasbihin (سبحان الله والحمد
لله ولااله إلا الله والله أكبر) sau xaya, ko kuma ya karanta (سبحان الله) sau uku, kana ya yi ruku'u ya
aikata kamar yadda ya yi a raka'o'in da suka gabata.
[2] Kashuf Gummati na Arbali. Babin
ambaton Imamu Aliyu. Da kuma Nafahatun Minas sira, na Mu'assatul Balahg
Comments
Post a Comment