MAULIDI BIDI'A KO SUNNA?



MAULIDI
BIDI'A KO SUNNA?















NA


HUSSAIN MUHAMMAD (BABALLE)










Hakkin Mallaka (m) Hussain Muhammad (Baballe)


An fara bugawa: 17/3/2008
An sake bugawa: 26-2-2009





ABUBUWAN DA KE CIKI

1 -  Gabatarwa...........................................................
2 – Mece ce bidi’a………………………………  5
3 – Bidi’a a wajen malaman Musulunci………… 7
4 – Manzon Allah mafi kyawun dabi’u…………15
5 – Maulidi bidi’a ne? …………………………..26
6 – Fa’idojon maulidi …………………………...32
7 – Yanka ragon suna …………………………...66
8 – Soyayyar manzo cikin Al-Kur’ani …………..39
9 – Soyayyar manzo a cikin Hadisi ……………...40
10 – Abin Lura …………………………………..52
11 – Mai son hadin kai shi ne Ahlissunna ………54
12 – Abin mamaki (1) …………………………...56
13 – Abin mamaki (2) …………………………...70
14 – Rage son Annabi …………………………...74
15 – Shubuha …………………………………….85
16 – Ibni Taimiyya da son Annabi ……………....88













GABATARWA
Godiya ta tabbata ga Ubangijin halittu, shi kadai yake ba shi da abokin tarayya, wanda in ka gode masa a kan ni'imar da ya yi maka sai ya kara maka wata.
Tsira da amincin wadanda ba su da iyaka kamar yadda ikonsa yake, su kara tabbata ga bawansa, annabinsa, ma'aikinsa mafi soyuwa a gare shi a kan dukkan halittu, wanda shi da kansa ya ce: "Mun daukaka ambatonka", wanda dominsa ne duk wani mai daukaka ya sami daukaka, shi ne Muhammadu dan Abdullahi (s.a.w.), da 'ya'yan gidansa tsarkaka da sahabbansa managarta.
Dalilin rubuta wannan littafi bai wuce na fadakar da 'yan uwa Musulmi, musamman dalibai a kan wata magana da ba matsala ba ce, amma ana nema a yau a mayar da ita matsala, wannan kuwa ita ce maulidin Manzon (s.a.w.) bidi'a ne ko sunna.
Sakamakon irin farin cikin da ‘yan uwana Musulmi masoya Manzon Allah (S.A.W) suka nuna ne, ya kara min kaimin inda na kara fadada littafin  akan yadda na yi shi da farko, da  wasu abubuwan da ban kawo a bugun farko ba.
Ina mika godiyata ga Mu'assasatu Rasulul A-Azam, musamman Sheikh Nur Muhammad Das da sauran Malamaina.
Ina mika godiyata ga abokaina da suka taimaka mini kamar   Isa Hassan sauransu.
Na kammala rubuta wannan littafi ranar 27/12/2007.Hussaini Muhammad Kamaye (Baballe)
GSM: 08037016673 / 064969871.


TAMABAYA!
SHIN MAULIDIN ANNABI (S.A.W) BIDI'A NE KO SUNNA?
Mece ce Bidi'a? Kuma mece ce Sunna?
Da farko dai ya kamata mai karatu ya san mece ce Bidi'a? Bidi'a kalma ce ta Larabci, wacce asalinta daga (bada'a yabdi'u bid'atan). Wannan kalma tana da isdilahin malamai.
Zan fara kawo mana ma'anarta ta lugga (ta asali). Kalmar bidi'a a asali (lugatan) tana nufin farar wani abu, wanda babu shi ko kirkirar wani abu wanda babu shi, kamar inda Allah ta'ala yake fada a cikin alkur'ani mai girma; "Ba ka kasance kai ne farkon aikowa ba daga ma'aikan Allah" (Manzanni).

BIDI’A

“KUL MA KUNTA BIDI’AN MINARRUSULI”
(( قل ما كنت بدعا من الرسل)) [1]
A wani wurin kuma Allah ya ci gaba da fada a cikin littafinsa mai girma; "Lallai Allah shi ne ya fari sammai da kassai (ya kirkiresu).
“BADI’USSAMAWATI WAL ARDI”.
((بديع السموات ولأرض)) [2]
Kalmar bidi'a ta sake zuwa a cikin Alkur'ani, inda Allah yake cewa Sahabban Annabi Isa su suka fare ta (kirkire ta).
“WA RAHABANIYYATN IBTADA’UHA”
((ورهبانية ابتدعوها)) [3]
Ya dan uwa mai karatu, ko a nan na tsaya ka iya fahimtar me kalmar bidi'a take nufi a dunkule, a asalinta na lugga.
To yanzu kuma zan kawo maganganun da malaman Musulunci suke yi a kan me kalmar bidi'a take nufi, idan an yi mata filla-filla. Wato mu ji ya ya suka fahimci wancan hadisi na Manzon Allah (S.A.W)
Ya zo cikin hadisin Manzo (S.A.W) yana cewa: .
“MAN AHDASA FI AMRINA HAZA, MA LAISA MINHU FA HUWA RADDUN”.

((من احدث فى امرنا هذا ماليس منه فهورد))
Sannan kuma gida nawa wannan kalma ta bidi'a ta kasu a wajen malaman Musulunci da Sahabban Annabi (s.a.w.)
Babu kokwanto a wurin duk Musulmi cewa bidi'a haramunce da fadin Manzon Allah (s.a.w.), wanda Allah ya shaide shi da cewa ba ya magana a kan son zuciya:
((وماينطق عن الهوى)) [4]





BIDI'A A WAJEN MALAMAN MUSULUNCI
Wadannan malaman da zan kawo maganganunsu a kan yadda suka kalli bidi'a a gaba, dayansu malaman Musulunci ne da aka hadu a kan gaskiyarsu, kuma sun taka rawa a wannan addinin namu na Musulunci, ta yadda idan a yau da wani zai yi musun gaskiyarsu to kamar ya rusa addinin ne gaba daya.
Malami na farko da zan kawo shi ne: Ibni Rajab Al-Hambali, a cikin littafinsa mai suna Jami'ul Ulumi Hikam, wanda aka buga a madaba'ar Hind. Ya ce: "Bida'a shi ne abin da aka fare shi, ba ta da asali a cikin shari'a ba, ko kuma ba a sami abin da za a dogara da shi ba a shari'a.
Amma abin da yake da madogara wannan ba a kiransa bidi'a, ko da kuwa zai kasance bidi'a ne a lugga (da ma'anar sabo abu).
2- Ibni Hajar Al-Askalani, wanda ya yi wa Sahihul Bukhari Sharhi, ya ce bidi'a shi ne abin da ba shi da asali a shari'a, kuma aka sanya shi a shari'a, sannan ya kasance ya yi karo da shari'a, wannan ita ce bidi'a abar zargi.
Za ka sami wannan maganar a cikin littafin Fatahul bari, Mujalladi na (5/ 56/17/9).
3- Imamu Shafi'i, Allah ya yi masa rahama, ya ce "Bidi'a ta kasu kaso biyu. Ta daya ita ce; Wacce ta saba wa sunnar Manzon Allah (s.a.w.) da littafin Allah da ijma'in malamai, wannan ita ce bidi'a, wacce take haramtacciya.
Ta biyu: Wacce aka fare ta ba ta saba wa daya daga cikin wadancan abubuwan da muka ambata ba, ita ce bidi'a wacce take halas".
Imamu Gazzali ya ce "Ba duk abin da aka fare shi bayan Manzon Allah (s.a.w.) ne yake zama abin da aka yi hani a kansa ba, abin da aka yi hani a kansa shi ne bidi'a wacce take kishiyantar Sunna tabbatacciya, ta wani al'amari a shari'a, tare da wanzuwar cutarwarsa.
Ya ci gaba da cewa "Kai, farar wani abu (kirkirarsa) yana zama wajibi idan dalilai suka sassauya".
Za ka iya samun wannan magana a cikin littafin Ihya'u: 2/3. Wanda aka buga a madaba'ar Al-halbi.
Ya dan uwana mai karatu, ka dubi kadan daga cikin maganganun malamai a kan mece ce bidi'a? kuma ya ya take? Wanda idan ka dauki magana daya daga cikin maganganun malaman nan ka dube ta, to za ka iya tambayar masu tada jijiyoyin wuya akan don me al'ummar Musulmi suke yin maulidin Annabi (S.A.W)
Shin ba su san da ire-iren wadancan maganganu da malamai suka yi ba ne? Ko kuwa a'a sun sani!
To idan za mu dauki maganar Imamu Gazali Allah ya yi masa rahama, inda yake cewa "Wani lokaci farar wani abu a cikin al'umma yana iya zama wajibi” (kirkirarsa). Za mu iya gaskanta shi daga wadannan misalan da zan kawo. Duk da yake shi kawai ya ce idan dalilai suka cancanza suka jirkita. Mai yiwuwa mai karatu ya ce shi ya ji kuma ya yarda maulidi na da kyau, to amma da ya halatta me ya sa sahabbai ba su yi ba? Ko kuma ya ce "Ai Manzon Allah (S.A.W) ya ce:
"Mafi alherin karni karnina, sannan wanda yake biye da shi, sannan wanda yake biye da shi''. Kuma duk karnonin nan uku ba su yi maulidi ba, to wannan Magana sai mu ce shaci fadi ce, tabbas magabata sun yi mauludin ma’aikin (S.A.W), kamar yadda dalilai za su zo nan gaba.
Mai karatu bari  na kawo maka kadan daga cikin maganganun magabata da suke nuni da magaba sun yi maulidi.
Na farko hatta dan Taimiyya ya yarda da maulidin Annabi, har ma yake cewa “Duk wanda ya yi maulidi ba da nufin koyi da Nasara ba, to zai sami ladan yin hakan, saboda soyayyarsa ga Manzon Allah (S.A.W). wannan Magana akwai ta a cikin littafin Ibni Tamiyya mai suna Ikitida’u Siradul Mustakim Mukalafati Ahlul Jahim.
Duk wani gungu na wadanda  suke sukar maulidi, su jikoki a akida ga dan Tamiyya toga abin daya ce.
Ka da ka yi mamaki mai karatu don ka ji wadannan gungun da suka rada wa kansu suna Ahalussunna, idan ka waiwaya baya a tarihin bayyanarsu a nan kasar, wasu daga cikinsu sun yi musun samuwar sharifai, saboda su a ganinsu babu sauran sharifai jinin Manzon Allah (S.A.W), don haka kada ka yi mamaki saboda duk  wanda ya karanta tarihin wannan addinin na Musulunci bayan wafatin (S.A.W) zai iya sanin halin da Ahalu-Baitin Manzon Allah (S.A.W) da wasu sahabbansa suka samu kansu na kora da tsangwama.
Amma ba za ka taba jin wancan gungun da yake haramta maulidi yana magana a kan wadancan mutane ba. Da ka yi maganar falalar Manzo ko ta Ahlul Baitinsa ba zai iya hakuri ba, sai ya yi Magana. Sai ya ce kana zuzuta abin, idan hadisi ne ka kawo ko da daga Sahihul Bukhari ko Muslim ka dauko zai ce maka bai inganta ba, balle ka fada masa wani littafin na musulunci.
Kai duk mai karatu ko kuma na ce mai yawan karantce-karance zai iya yarda idan na ce har litattafai irin wadannan gungun masu hana maulidin ba su bari ba, za ka iya ganin littafin a wani waje idan ka sayo irinsa domin ka ga wata magana da aka yi a kan Manzon Allah (S.A.W) ko kuma a kan Ahlul Baiti sai ka zo sai ka ga sam-sam babu wannan maganar a naka littafin da ka sayo. Ko ka san dalili hakan?
Dalilin shi ne, har abin ya wuce a ce al’umma ka da su yarda akwai sharifai da waliyai, har ta kai suna cire abin da yake cikin wasu litattafai. Mai yiyuwa mai karatu idan bai taba cin karo da haka ba ya ce hakan ba zai yiwu ba.  Ko kuwa idan tunaninsa bai kai nan ba ya ce ka ji, to yaya ma za a yi littafin da aka rubuta shekara sama da daruruwa a ce wasu za su cire wani abu?
To sai na ce da kai ga misali: Ka sami wannan littafin da dan Taimiyya ya yarda da halaccin yin maulidi, idan ka sami wanda aka buga shi a Saudi Arebiya za ka nemi waccan maganar da mawallafin ya yi babu ita an cire ta. Sanan kuma idan ka duba littafin Ahzab wa Aurad wanda shehu Ahmadu Tijjani (r.a) ya wallafa za ka ga irin waccan ha’incin na cire wasu abubuwa daga cikin.
A cikin littafin Shehu Tijjani ya kawo wasu bayin Allah wadanda duk jikokin Manzo (S.A.W) ne, kuma ya yi kamun kafa da su, amma yau idan ka samu sabon bugun littafin ba za ka gani ba su ma an cire.
Duk wadannan abubuwan da suke faruwa, wadanda suke yinsa ko suke jagorantarsa babu kunya babu tsoron Allah, wai sune Ahalissunna, sauran musulmi kuma sun sa musu sunayen da suke so, kamar yadda  ka karanta a baya. Don haka ko da ka karanta wata magana na ce za ka same ta a littafi kaza shafi kaza, idan ka duba shafin in ba ka gene ba ka ci gaba da dubawa, saboda akwai bambancin madaba’a. Idan kuma duk da haka ba ka gani ba ka nemi tsohon bugunsa za ka samu.
Ni dai fatana Allah ya sa masu irin wannan dabi’a su daina su nutsu, Allah ya hada kan al’ummar musulmi a duk inda suke. Allah ina tawassuli (kamun kafa) da Manzonka (S.A.W), ka sa wannan littafi ya amfanar a al’ummar Manzo (S.A.W). Allah ina tawassuli da tausayi da rahamar da ka suffanta mafi soyayyarka da su (S.A.W) da ka karbi wannan dan littafi da na rubuta, Allah domin matsayin wannan Manzo wanda duk annabawanka da manzanninka suka zo domin share masa fage.
Mai karatu bari ka ji daga ciin manyan sahabban Manzo (S.A.W), Ibni Jauzi ya kawo a cikin littafinsa mai suna Al-Hisni wa idatul hisni, sannan Shaukani ya kawo a ciin littafinsa mai suna Tuhfatuz Zakirin, sannan Ibni Ja’ad shi ma ya kawo wannan hadisin da zan kawo wa mai karatu yin tawassuli da Manzo bayan wafatinsa. Ya tabbata, Abdulahi dan Umar (r.a) ya yi kamun kafa da Manzon Allah da lafazin “Ya Muhammadu! Wanda yin hakan a wajen wasu haramun ne.
Kuma shirka ne. Domin sanin wannan hadisin  mai karatu zai iya duba Tuhfatuz Zakirin, shafi na (267), Musnadu ibhni Da’aj shafi na (369).
Amma su masu haramta maulidi,  suna cewa duk wanda ya mutu ba zai amfanar da kai ba da komai saboda ba ya jinka kuma ba ya ganinka! To ga wani hadisi daga Anas, ya ce Manzo (S.A.W): Annabawa a cikin kaburburansu masu sallah ne, ma’ana suna yin addu’a. wannan hadisi Baihaki ya inganta shi a cikin juzu’in da yake magana a kan rayuwar annabawa bayan wafatinsu hadisi na (15), Alhafiz ibni Hajar ya kawo a cikin Fatahul Bari, mujalladi na shida shafi na (487), ya tabbata hadisin da yake cewa: Babu wani mutum musulmi da zai wuce kabarin dan uwansa musulmi wanda ya san shi a nan duniya ya yi masa sallama sai na cikin kabarin ya san wannan mutumin, kuma ya  mayar masa da sallamar. Alhafir Abdul Hakki Al’ishbili ya inganta shi a cikin littafinsa Al’Adabul Mufrad, halaccin  kiran Manzo (S.A.W) domin biyan wata bukata bayan wafatinsa.  Yin hakan a wajen wasu shirka ne.
Bukhari ya kawo cewa: Wani mutum ya wuce ta wata makabarta da daddare, sai ya ji sauti daga wani kabari ana karanta suratul Malik har zuwa karshenta. Da ya wayi gari sai ya bai wa Manzo (S.A.W) labari. Sai Manzo (S.A.W) ya ce: “Ai tana hana azaba, kuma tana  tseratarwa.” Siyudi ya kyautata wannan hadisin, ka duba Jami’us Sagir mujalladi na biyu shafi na (56).
 Amma duk da wannan hadisan a wajen mai haramta maulidin Annabi, haramun ne ka yi kamun kafa da Manzo (S.A.W), wai duk don su  nuna maka  cewa shi fa Manzon nan, mutum ne kamar sauran mutane!
To idan har ya kasance wanda yake cikin kabari yana jin sallamar dan uwansa mumini, to ina ga waliyan Allah da Annabawansa, balle ka je ga shugaba (S.A.W).
Mai karatu daga nan za ka gane  cewa lallai mai sukar maulidi,  yana so ya cire maka jin cewa za ka iya yin kamun kafa da  Manzo (S.A.W) a kan wata bukatarka kuma ta biya. Da kuma yin bai halatta ba da Abdullahi dan Umar (r.a) bai yi ba, da sauran hadisan da  suka gabata da ba su tabbata ba. Kai, al’amarin kamun kafa da Manzo (S.A.W) bayan ya yi wafati abu ne wanda yake a bayyane a tsakanin al’ummar da  da ta yanzu, inda za ka san haka hatta dan Taimiyya wanda suka yi masa lakabi da Shaikhul Islam ya kawo wancan hadisin na Abdullahi dan Umar  (r.a) a cikin littafinsa mai suna Kalimud Dayyib, shafi na (73) ya ce hadisi ne ingantacce. Ka ga har dan Taimiyya suna mushirikantar da shi ba tare da sun sani ba, wanda shi ne kakan dan Abdul Wahhabi a akida, to ka ga a she ko mutum ya ce maka shi ba Bawahabiyye ba ne ko ma ya canza riga ya ce maka shi Basalafe ne ko Ahlissunna ko ma mai zai kira kansa, tunda dama shi yake rada wa kansa suna sai ya fara karyata hadisin da kakansa na akida ya ce ya inganta, kafin ya zo ga na sauran Musulmi wanda su dama sun yarda da haka ba a baki kawai ba.
To mai karatu abin mamaki ba ya karewa, ta ya ya idan ka ce :Ya Muhammadu ko kuma ya Rasulallahi ko Agisni zai zama shirka, amma kuma kiran wani ya zama abu mai kyau! Mutum zai iya kamun kafa da ayyukansa da ya yi na kirki zuwa ga Allah, zai iya kamun kafa da sallar da ya yi ko kuma azumin da ya yi, ko da waliyan Allah ko kuma bayin Allah na gari. Ya tabbata Annabi Adamu (A.S) ya yi kamun kafa da Manzo (S.A.W) inda ya ce: “Ya Allah ina rokonka, domin matsayin Muhammad ka gafarta mini. Ka duba Sunani ibni Maja mujalladi na daya shafi na (261), Musnadu Ahmad mujalladi na uku shafi na (3) hadisi na ashirin da daya.
Wato idan za ka bibiyi litattafai za ka sha mamakin wadannan mutane, wanda su babban burinsu duk inda suka leka su ka ga al’ummar Manzo (S.A.W) a hade sai su daidaita ta.





MANZON ALLAH (S.A.W) MAFI  KYAN DABI’U
Allah yana cewa: (Duk abin da Manzo ya zo muku da shi ku rike shi, abin kuma da ya hane ku to ku bar shi)
Da farko kamar yadda Imamu Gazzali ya fada, idan dalilai suka canza ko suka jirkita suna sa wa ya zama wajibi a kan al'umma kirkirar sabon abu. Ko ba komai dan uwa mai karatu ka san Manzo (s.w.a.) ya ce, an yi masa karya yana raye, kuma za a yi masa bayan rasuwarsa, kuma duk wanda ya yi masa karya yana sane, ya tanadi mazauninsa a wuta.
To yau mu al'ummar Musulmi mun wayi gari a wani lokaci da ban san ina tunaninmu ke tafiya ba, ta yadda idan za ka dauki wani littafi ka karanta za ka iya cin karo da hadisan da ake danganta su ga Manzon Allah (S.A.W), wanda kai ko limamin unguwarku ne aka danganta masa wannan maganar, a matsayinka na mai hankali, kuma masoyin wannan malami za ka ji babu dadi.
To amma lokaci guda, saboda an ce hadisi ne shi ke nan ka ji kuma ka bi. Lallai ya zama dole biyayya ga maganar Manzon Allah (S.A.W) ga duk mai shaidawa da kalmar shahada.
Abin tambaya a nan shi ne, duk abin da aka ce Annabi ya yi hakan ne ya yi din ko kuwa?
Misalin wani mai karyar bin sunnar Manzon Allah (S.A.W) zai iya ce maka: Akwai hadisin da Manzon Allah ya yi fitsari a tsaye, kuma a akan juji (bola). To saboda Allah idan Manzon Allah Annabi Muhammad (S.A.W) ka ke bi, kuma ka ke koyi  da shi, kuma kana karanta Alkur'ani mai girma, kana kuma fahimta, kai ko ba ka iya fahimtar ayoyin da ka ke karantawa, ta ya ya waccan magana za ta sami gindin zama a zuciyarka, har ka ji ka nutsu da ita.
Manzon Allah Annabi Muhammad dan Abdullahi (S.A.W) shi ne fa wanda Allah da kansa ya ba shi shaida, in da yake cewa: "Lallai kana kan dabi'u masu girma".
((و إنك لعلى خلق عظيم))[5]
To amma ga wasu sun kawo hadisi wai wanda Allah ya yi wa shaida irin wannan, kuma shi za a dangantawa waccan mu'amalar (yin fitsari a kan bola), kuma wai har ka sami wani musulmi ya yarda. Kai abin da mamaki ga wadanda suke da irin wannan tunani. Kai, ko da malamin da ya karanta maka wannan hadisin ka samu mabiyansa ka ce da su; "Ni kuwa akwai ranar da muke tafiya da malam, sai ya ji fitsari ya kama shi, sai muka tsaya daidai wata bola (Juji), sai ya hau kan bola, ya fito da al'aurasa ya yi fitsari akan bola a tsaye. In dai har ba ku yi rigima da su ba to zai zama mafi karancin abin da za su iya ce maka shi ne makaryaci. Saboda ya saba da dabi'u masu kyau, a ga mutumin kirki ya fito da al'aurarsa waje ya tsaya a kan juji ya yi fitsari a tsaye.
Wannan fa ga irinmu ya-ku-bayi muna jin bai kamata ba, to ina ga Manzon Allah (S.A.W), wanda Allah ya yi wa wancan bayani!
Kuma ma ai abu ne sananne Manzon Allah (S.A.W)  babu wanda ya kai shi kunya da kamewa da tarbiyya. Manzon Allah (S.A.W) ya ce "Ubangijina ya tarbiyyantar da ni, ya kuma kyautata tarbiyyata".
((ادبنى ربي فأحسن تأديبي))
To, ko wannan kawai muka duba, ya isa dalilin da zai sa mu ware wata rana domin mu karanta wa yaranmu da mu manyan dan abin da Allah ya sanar da mu, dangane da Manzon Allah (S.A.W), saboda sanin Manzon Allah (S.A.W) sai wanda ya yi shi, shi ne ya san hakikaninsa, don haka sai muka ga a cikin ranekun wace rana za mu dauka, sai muka ga ranar haihuwar Manzon Allah (S.A.W) ita tafi dacewa da mu dauka, musamman idan muka dubi ayoyin da duniya ta shaida sun faru ranar haihuwarsa (S.A.W).
Sai mu yi amfani da wannan ranar, domin yawaita ciyarwa sama da yadda muke yi a sauran raneku, mu taru muna farin ciki muna masu ziyartar 'yan uwanmu, mu yalwata ga talakawanmu, mu yi sababbin dinkuna, mu karanta wa yaranmu darajojin Manzon Allah (S.A.W), ta yadda ko da sun ji ire-iren wadancan maganganu (fitsari a tsaye) za su san maganganu ne da makiya addinin Musulunci suka zo da su, domin su rage mana ko su raunana mana imaninmu ta hanyar rage ganin kimar Manzo (S.A.W).
Sahihu Muslim ya kawo hadisi:
1.    Daga Aba Hurairata (R.A) Ya ce: Annabi Muhammad (S.A.W) ya ce: “Wanda ya yi kira zuwa ga shiriya zai kasance yana da lada gwargwadon ladan wadanda suka bi shi, ba tare da ladan da aka ba su ba ya ragi nasa ladan ba da komai.
Haka wanda ya yi kira zuwa ga bata, zai kasance yana da zunubi gwargwadon wadanda suka bi shi, ba tare da zunubin da aka ba su ya rage yawan nasa ba.”
Wannan hadisi yana nan a cikin musulim, mujalladi na takwas, cikin kitabul Ilmi, shafi na sittin da biyu (62).
2.      Sahihu muslim ya karbo daga Jarir dan Abdullahi (r.a), ya ce: Wanda ya sunnanta wata sunna a cikin muslunci kyakkyawa, kuma aka yi aiki da ita bayansa, za a rubuta masa ladan wanda ya yi aiki da ita, ba tare da an rage wani abu daga cikin ladansa ba.
Haka kuma duk wanda ya sunnanta wata sunna  mummuna, aka yi aiki  da ita a bayansa, shi ma za a rubuta masa zunubi gwargwadon wadanda suka yi aiki da ita, ba tare da an rage wani abu a zunubinsu ba.
Mai karatu zai iya samun wannan hadisi a cikin sahihu Muslim, mujalladi na takwas, Kitabul Ilmi, shafi na sittin da daya (61 zuwa 62). Manzon Allah (S.A.W) ya yi gaskiya.
Mai karatu ka dubi wadannan hadisai da kyau da idon basira, ba kallon da idanuwa kawai suke kallo ba. A’a, kallon fahimta, a matsayinka na wanda Allah ya yi wa baiwa da ni’imar da duk wanda ba shi da ita ko kuma ya rasa ta, to fa duk abin da zai yi shari’a ta dauke masa hukunci (alkalami), wannan ni’ima kuwa ita ce: Ni’imar hankali, saboda duk wanda ya rasa hankali to wannan ya yi asarar da ba ta misaltuwa.
Tun da kuwa haka ne, kai da Allah ya yi wa hankali, ya shiryar da kai adinin Musulunci, ya ba ka lafiya, ya ba ka damar da bai ba wasu ba, misali kamar baiwar karatu da rubutu, za ka iya rubuta magana kuma za ka iya karantawa, amma abin mamaki  duk wadancan baiwoyin da Allah ya yi maka ba ka ganinsu, balle ka yi amfani da su, sai dai duk wanda ka ke ganin shi ne malaminka sai ka mayar da shi shi ne jinka, shi ne ganinka, shi ne kuma tunaninka, ko da tunaninka da abin da ka ke fahimta da hankalinka sun ce maka wannan abin fari ne to sai ka jira malaminka ya ce da kai fari ne.
Amma in da zai ce da fari baki ne ko kuma ja ne ko shudi ko kuma ba haka ba ne, to maganarsa za ka bi!
Misali: Za ka iya ganin haka idan Allah ya sa ka taba cin karo da mai haramta Maulidin fiyayyen halitta Annabi Muhammad (S.A.W). shi wannan mutum akwai abin mamaki a tare da shi, idan ka ce an yi duniya da lahira domin Manzon Allah (S.A.W), zai ce kai karya ne! amma zai iya ce maka mahaifan Manzo(S.A.W) ‘yan wuta ne ko ya ce da kai ba a ce a so Manzon Allah (S.A.W)ba  an ce a bi shi ne, wai dole dai sai ya cire maka soyayyar da ka ke wa Manzo(S.A.W), ka bi abin da yake so.
Idan za ka yi maganar hadisi zai ce maka shi ne ya fi kowa riko da hadisin Manzon Allah (S.A.W), zai ce maka shi ya fi kowa karanta hadisai.
To mai karatu ina so ka yi wa kanka hukunci na adalci, idan har mai ganin ka kebance wasu ranaku a cikin watan da aka haifi Manzon Allah (S.A.W), ka raya su domin tunawa da Manzon Allah (S.A.W)da karanta tarihinsa, ya zama bidi’a, kuma yin hakan ya zama haramun, saboda Manzon Allah(S.A.W) bai yi ba, to me zai hana mai wannan tunanin ya haramta sallar tarawihi (Asham)?
Wacce ake yi a cikin watan Ramalana , saboda har yanzu ban taba ji ba, kuma ban karanta ba, a ce ga wani hadisi wanda ake danganta shi da Manzon Allah (S.A.W) ko mai raunin hadisin da aka ce Manzon Allah (S.A.W) ya ce ka da a yi maulidinsa, ranar tunawa da ranar da aka haifi Manzon Allah (S.A.W) ko ya ce bidi’a ne.

RAYA ALAMOMIN ALLAH
MAULIDI NE
Idan muka dauki ranar aikin hajji gaba dayanta, Allah madaukakin sarki ya sa ta ne domin ta zama ranar raya  al’amuran wasu manyan bayinsa. Misali kamar:
1 – Ka dauki Makamu Ibrahim (A.S).
2 – Allah madaukakin Sarki ya umarci mutane da su nemi tabaraki, su yi kamun kafa da wurin da Annabi Ibrahim ya taka da kafafunsa, a cikin haraminsa mai alfarma kuma duk shekara. Kuma Allah ya umarce mutane da su rike shi wajen sallah, domin raya al’amarin Annabi Ibrahim (A.S), wannan bai zama tarayya da Allah ba, kuma bai zama an dauki Annabi Ibrahim (A.S) a matsayin abin bauta ba.
3 – Safa da Marwa da Allah madaukakin Sarki ya yi bayaninsu a cikin Alkur’ani, ya ce: “Lallai Safa da Marwa suna daga cikin alamomin Allah.
(إن الصغا والمروة من شعائر الله)[6]
Suratul bakara, aya 158.
Idan ka dauki Sayyida Hajara waliyiyar Allah ce, sai ga shi tafiyar da ta yi ta hau dutsen Safa ta sauko ta hau dutsen Marwa domin neman ruwan da za ta shayar da danta Annabi Isma’il (a.s.) sai Allah ya mayar da shi ibada saboda raya al’amuran waliyiyar Allah matar Annabin Allah (A.S)
Ranar haihuwar Manzon Allah tana daga cikin alamomin Allah, wannan kuwa ba na tunanin mai ganin maulidi a matsayin haramun ko malamansa za su iya musun abubuwan ban mamakin da suka faru saboda haihuwar Manzon Allah (S.W.A.), wannan ba sai na kawo su ba saboda haihuwar Manzon Allah (S.W.A.), da abubuwan da suka faru wadanda manya-manyan alamomi ne na tabbatar da samuwar Allah da buwayarsa, da kuma nuni da girman abinda aka haifa, shi ne Manzon Allah (S.W.A.). To ko wannan kawai ta ishi mai yin maulidi hujjar yin maulidi. Idan haihuwar Manzon Allah ba ta daga cikin alamomin Allah to ya kamata a taimake ni a matsayina na dalibi, a sanar da ni, zan so hakan sosai, tunda dai Allah cewa ya yi, alamomin Allah: "LALLAI SAFA DA MARWA SUNA DAGA CIKIN ALAMOMIN ALLAH". Bai ce su kadai ne alamomin Allah ba, balle wani ya ce mu dai safa da Marwa aka ce! A'a cewa yayi suna daga cikin alamomin Allah.
Yau muna murna muna farin ciki, muna godiya ga Allah ta hanyar yawaita karatun Alkur'ani, da yawaita sadakoki da yawaita salati a gare shi (S.W.A.) kamar yadda ka yi salati kai da mala'ikunka a gare shi (S.W.A.), kuma ka umarci wadanda suka yi imani su yi masa salati. Allah ka yi tsira da aminci ga mazonka da alayensa kamar yadda ka yi tsira ga Annabi Ibrahim (A.S.) duk wannan godiya ce a gare ka ya Allah saboda ni'imar da ka yi mana ta sanya mu cikin al'ummar Manzonka dan Abdullahi (S.W.A.).
Domin ka ka ce:
((وأما بنعمة ربك فحدث))
Allah mun gode maka godiya kan godiya wacce ba za ta kare ba har sai rayiwarmu ta kare.
KIRA GA MAI SUKA
Kira ga mai sukar maulidin Annabi (S.W.A.), da ka yi tunani ka koma makaranta saboda ka gane cewa Manzon Allah (S.W.A.) soyayyarsa ta fi komai dadi a wannan rayuwa, don haka gwargadon soyayyarka da Manzon Allah (S.W.A.) gwargwadon ganin girmansa. Soyayyar Manzon Allah za ta iya sa masoyinsa ya rabu d komai saboda shi, kamar yadda al'amarin yake, duk yadda kuka kai ga kin junanku to soyayyar Manzon Allah (S.W.A.) za ta iya hada ku ku zama 'yan uwan juna.
Manzon Allah ya yi gaskiya, saboda dama ya ce: "Lallai akwai wasu mutane daga cikin alummata, za su zo a bayana, dayansu zai so ya ganni, ta yadda da zai sayi ganina da iyalansa da dukiyarsa da ya yi hakan".
((إن أناس من أمتي يأتون بعدي يود أحدهم لو اشترى رؤيتي بأهله وماله))
Don haka nake cewa da mai sukar maulidi, ya yi hakuri, domin ya fi masa alkhairi, saboda mu Manzon Allah (S.W.A.) ya fi komai namu da mu kanmu, don haka kullum soyayyarsa sai karuwa take yi a zukatanmu, kuma kullum muna nuna wa 'ya'yanmu matsayin Manzon Allah ta hanyoyi daban-daban. Daya daga ciki ita ce hanyar yunkurinmu a kan mu kyautata wa iyalanmu, mu yi sababbin dinkuna idan muna da hali, mu dafa abinci mu raba wa al'umma har ma wanda ba musulmi ba ya ci, saboda albarkacin Manzon Allah (S.W.A.).
Kamar yadda muka sani, soyayya ba ta takaita a zuci ba, a'a, dole ne a ga abin a fili a aikace. Ka iya cewa misalin imani da bayyanarsa a fili kamar ka kunsa wani abu ne wanda yake da maiko, kamar kosai ta takarda; Dole sai ka ga maikon ya naso bayan takardar.
Abin da nake so a fahimta a nan shi ne: Dole ne duk wanda ya yi imani da Allah da Mazonsa sai ka ga alamar haka a tattare da shi. Tunda yana daga cikin soyayya a ga alama a aikace a jikin ma'abocinta.
Idan kana son Allah da Manzonsa, to dole ka lazimci biyayyarsu da gudun saba musu.
So yana da alamu bayan biyayya, sannan kuma yana da tsari da yake bayyana ga ma'abocinsa. Za ka ga masoyi na ziyartar masoyinsa, yana kuma girmama shi, yana kare shi daga dukkan wani abin da zai cutar da shi ko ya kaskantar da shi idan masoyin yana raye.
Idan kuma ya rasu ko kuma kun rabu da shi za ka yi bakin ciki mai tsanani. Daga cikin abin da ke bayyana bakin ciki akwai zubar da hawaye, kamar yadda Annabi Yakuba (A.S.) ya yi, saboda rabuwar da ya yi da masoyinsa Annabi Yusufa (A.S.).
Haka Annabi Yakuba ya ci gaba da zama cikin bikin ciki da zubar da hawaye saboda rabuwa da masoyi, har sai da ta kai idanuwansa sun yi dusu-dusu.
Soyayya na sanya masoyi kula da iyalan masoyinsa, ya rinka girmama su ta hanyar gwada su saboda kyautatawa masoyinsa, kamar yadda zai rinka girmama 'ya'yansa ya yawaita yi masa addu'a, ta yadda duk shekara zai raya ranar haihuwa masoyinsa da kuma juyayin ranar mutuwarsa.
Son Manzon Allah ya zama dole a kan duk mumini.
Abin nema a nan shi ne, ba wai so wanda zai tsaya a zuci kawai ba, a'a, so wanda zai bayyana hatta a harkokin mutum na yau da kullum. Dole ne a ga alama ta son Manzon Allah (S.W.A.).
To idan ka dauki kissar Annabi Yakuba (A.S.), ashe ya halatta ga dukkanin musulmi ya dauki kowace irin hanya matukar ba ta saba wa shari'a ba domin ya bayyanar da soyayyarsa ga Manzon Allah (S.W.A.).
Sanin kowa ne akwai dan Zuhairu, wanda mawaki ne ga Manzon Allah, wanda bai takaita soyayyarsa ga Manzon Allah a zuci kawai ba, ko kuma ga horo da hani kawai, sai da ya bayyanar da ita a fili. Ta yadda ya yi wa Manzon Allah (S.W.A.) wakoki na yabo da dama; Wannan Ka'abu dan Zuhairu kenan.
Akwai irin su Hassan bin Sabit Al'ansari, wanda shi ma mawaki ne na Manzon Allah (S.W.A.), da sauran ire irensu da dama. Ta yadda da a ce wani zai dauki aikin tattara wakoki na yabo da aka yi wa Manzon Allah yana raye, kuma bai hana ba, to mutum ya yi litattafai da yawan gaske, saboda a wancan lokacin, yabon Manzon Allah ya yawaita sosai, fiye da yadda mai karatu yake tunani.
Kasdalani ya ce: Ma'abota Musulunci (Musulmi) ba su gushe ba suna yin maulidi na Annabi (S.W.A.), a duk watan Rabi'ul Auwal . Sun kasance suna yin sadaka a cikin dararensa da duk nau'o'in sadaka. Suna bayyanar da farin cikinsu, suna karawa a kan abubuwan da suka saba na Alkhairai, suna masu mayar da hakali wajen karanta abubuwan da suka faru a ranar haihuwar (S.W.A.), suna bayyana matsayinsa.
Ya ce (Al-kasdalani ya ce Allah ya ji kansa): Wanda ya dauki dararen watan haihuwars (S.W.A.) kamar ranar ido domin nuna farin cikins don zama mafi tsanani ga zuciyar wanda yake mara lafiya (mai haramta maulidi), wannan ciwo ne mai wuyar magani idan ka fahimci abin da na ambata, ba na zaton akwai wani mutum da zai yi shakka a kan halaccin maulidin Annabi (S.W.A.), wadanda a cikinsu yardar Allah da Manzonsa sun tabbata a fili, don haka bai inganta ba a kira maulidi bidi'a, idan mun lura da abin da muka karanta na cewa bidi'a ita ce wacce ba ta samo asali daga littafin Allah ba ko hadisan Manzon Allah (S.W.A.).
Sai dai in za a kira maulidi bidi'a luggatan kamar yadda bayani ya gabata, wanda yake da ma'anar sabo. Idan ka fahimci sabon abu kowanne a matsayin bidi'a, ba maulidi be kadai aka fare shi ba, wanda yake shi zan iya cewa ma kamar yadda ya tabbata a abin da ka karanta maulidi ba sabon abu ba ne, don haka ba za a kira shi bidi'a ba. Wannan da hujjoji da mai karatu ya karanta su a baya, kai har ma da hujjoji masu yalwa maulidi ba bidi'a ba ne.

MAULIDI BIDI’A NE?
Za ka yarda da ni idan na ce yin maulidi wata hanya ce daga hanyoyin girmama Manzon Allah (S.W.A.), da fito da darajojinsa da bayyanar da su a fili karara. Duk ayyukanka na alkhairi da ka ke yi ko ka ke niyyar ka yi yana nuna soyayyar Manzon Allah da farin ciki da debe kewa da daukaka ambaton Manzon Allah (S.W.A.).
Koyi da fadar Allah (S.W.T.): "MUN DAUKAKA AMBATONKA".
((ورفعنا لك ذكرك))
Sunnar Manzon Allah da take nuna ka yi murna da nuna farin ciki da zagayowar ranar haihuwarsa.
Imam Bukhari ya fitar a cikin littafinsa; An samo daga Umar bin Khaddabi (R.A.) ya ce: Wani mutum daga Yahudawa ya ce da shi: "Ya sarkin muminai, akwai wata aya a cikin littafinku da a ce a kanmu ta sauka mu Yahudawa to da mun riki wannan ranar a matsayin ranar idi.
Sai Sayyadina Umar ya ce: Wace aya ce wannan?
Sai bayahuden ya ce: Ayar da take cewa: YAU NE NA CIKA MUKU ADDININKU, NA KUMA CIKA MUKU NI'IMATA, NA YARDAR MUKU DA ADDININ MUSULUNCI SHI NE ADDINI.
((اليوم اكملت لكم دينكم وأتممت عليكم نعمتي ورضيت لكم الإسلام دينا)) [7]
Sayyadina Umar (R.A.) ya ce: "Lallai ni na san ranar da aka saukar da ita, da wurin da aka saukar da ita, Manzo yana tsaye a Arfa ranar Juma'a.
Sannan Tirmizi shi ma ya fitar da wani hadisi da ya zo daga dan Abbas (R.A.), ya ce: An saukar da ita ne ranar idi a ranar Juma'a, a kuma ranar Arfa. Tirmizi ya ce hadisi ne ingantacce.
A cikin wanann hadisin da Sayyidina Umar dan Khaddab (R.A.) ya dace a kan zaben ranar wata ni'ima a wannan rana ta zama idi, ta yadda zagayowar wannan rana zai sa mu yi wani abu mai kamar idi. Mu yi biki domin nuna farin cikinmu ga Allah saboda wannan ni'ima da yayi mana, da bayyanar da farin cikinmu da walwalarmu saboda waccan ni'ima. To ina ga ni'imar bayyanar Manzon Allah (S.W.A.), wanda yake rahama ne ga muminai (S.W.A.).
Sannan kuma mai karatu idan kana karanta Alkur'ani na san ka karanta ayar da Annabi Isa dan Maryam (A.S.) yake rokon Allah da ya saukar musu da wani kabaki daga sama, shi da sahabbansa domin ya kasance idi a gare su, kuma a kasance aya ce daga gare ka. Har zuwa inda yake cewa; kaine mafifici mai azurtawa. Sauratul Ma'ida.
((ربنا انزل علينا مائدة من السماء تكون لنا عيدا لأولنا وآخرنا وآية منك وارزقنا وأنت خير الرازقين))[8]
Alma'ida, aya (114).
To idan har Annabin Allah Isa (A.S.) zai mayar da wata rana da Allah ya saukar masa da kabaki daga sama, kuma wannan kabakin ya zama aya, saboda haka zai mayar da wannan rana idi, ranar nuna farin ciki, shi da sahabbansa saboda wannan aya. To mene ne zai hana mu mu al'ummar Manzon Allah mu yi maulidin sa (S.W.A.), mu nuna farin cikinmu da annashuwarmu da godiyarmu ga Allah saboda ni'imta mu da ya yi da babbar ni'ima (S.W.A.).
Saboda ni dai ban ga wata ni'ima da Allah ya yi ba wacce ta fi ni'imar bayyanar Manzon Allah (S.W.A.). Haka kuma ban gani ba ko na ji wata aya da ta faru ta zama tana dauke da al'amura na ban mamaki da nuna isarta ban mamaki irin abubuwan da suka faru ranar haihuwar Manzon Allah (S.W.A.).
Haka al'amarin yake, tabbas mun riki ranar da aka saukar da ni'ima wacce ta ke za mu ci abinci mu yi farin ciki a matsayin idi.
To haihuwar Manzon Allah ni'ima ce mai girma, wacce Allah ya yi wa al'ummar musulmi tagomashi da ita, to don me mu musulmi ba za mu dauke ta ranar bayyanar da farin cikinmu da annashuwarmu ba?

MANZO MAI FIFIKO
Lallai mun zabi mu fi ambatar shekarar da aka haifi Manzon Allah a kan shekaru, kuma mun zabi mu fi maimaita ambaton watan da aka haifi Manzon Allah a kan sauran watanni.
Mun zabi mu fifita ranar haihuwar Manzon Allah a kan sauran kamar yadda muka fifita Manzon Allah dan Abdullahi (S.W.A.) a kan dukkan abin da aka halitta, idanuwa ba su taba ganin wanda ya fi ka kyawu ba, mata ba su taba haihuwar wanda ya kai ka kyawu ba (S.W.A.).
An halicce ka ka ba ka da wata tawaya (naksu), kai ka ce kai ka halicci kanka kamar yadda ka so (S.W.A.).
أجمل منك لم ترقط عين
وأجمل منك لم تلد النساء
خلقت مبرءا عن كل عيب
كأنك قد خلقت كما تشاء
Idanuwa ba su taba ganin mai kyau kamarka ba.
Kuma mata ba su taba haifar wanda ya kai ka kyau ba, an halicce ka kubutacce daga dukkan aibi.
Kai ka ce kai ne ka halicci kanka kamar yadda ka so.
Daga cikin dalilan masu haramta maulidi suna cewa: Maulidi ibada ne daga ire-iren ibada, Muhammad Hamidu Alfakih ya ce: Yin Maulidi da zikirori wadanda suka cika garuruwa da sunan masoya, wannan wani nau'i ne na bauta musu da girmama su.
To a nan, mai karatu ya kamata ka dubi wannan magana da wasu masu mummunar fahimta suka doru a kai!
Duk musulmi ya san cewa duk abin da zai yi, da farko sai ya yi niyyar wannan abin ko ya dace ko kuma bai dace ba. Misali; Tun kana yaro mahaifinka ya sa ka a makaranta, to ka ga a nan shi ya sa ka da niyyar ka sami ilimi da tarbiyya don ka zama mutum na gari, wanda zamowarka mutum na gari shi ne babbar alamar da ke nuna cewa za ka rabauta a rayuwarka. Kuma mahaifinka da ya saka ka dama niyyarsa ke nan.
Sannan su masu irin wannan tunani ba su san cewa Allah yana kallon zuciyar mutum ba ne? ko kuwa ba su san dukkan aikin ba ya zama karbabbe sai da niyya ba? Don mutum ya yi dacen raya ranar da aka haifi Manzon Allah sai ya zama ya bauta masa ne? Ko kuwa ni da nake yin maulidin Manzon Allah (S.A.W) ban ce na bauta masa ba, sai kai ne za ka ce ina bauta masa, saboda ka rasa hanyar da za ka soke shi a shari'ance?
Kai zuciyarka ba ta da lafiya, har ta kai babban tashin hankalinka a rayuwa shi ne ka ji an ce watan haihuwar Manzon tsira Muhammad (S.W.A.) ya zagayo musulmi za su yi bukukuwa, domin nuna farin cikinsu da ni'imar da Allah ya yi musu ta haihuwar babbar ni'imar da Allah ya yi wa mutum da aljan, wacce ba a taba samun irinta ba, ba kuma za a sami irinta ba, wato ni'imar haihuwar annabi Muhammad dan Abdullahi (S.W.A.).
Kai kuma mai kin maulidi, watan musiba da bakin ciki ya kama a wajenka, saboda hakan ne ma, tun da ka yi duk iya abin da za ka yi ka ce yin maulidi bidi'a ne haramtacciya, ka rasa hujja ta hankali ko daga cikin Alkur'ani ko hadisan Manzon Allah (S.W.A.), wadanda suka inganta ta hanyar masoya Manzo na gaskiya, ba masu fada a baki ba, wadanda kullum idan ka ga sun zare takubbansu to babu inda za su saka shi sai a kan musulmi, wanda za ka ga duk inda suka sami musulmi to babban tunaninsu na farko shi ne, su raba kawunansu ta hanyar kiran 'yan uwanmu musulmi da sunayen batanci.





FA'IDOJIN MAULIDI
1.  Muna sabunta godiyarmu ga Allah da ya yi mu cikin al'ummar da ta fi kowace al'umma, saboda matsayin Manzon Allah (S.A.W), kamar yadda Allah ya fada a cikin Alkur'ani mai girma: "   KUN KASANCE MAFIFICIYAR AL'UMMA DA AKA FITAR  DAGA MUTANE, KUNA UMARNI DA KYAKKYAWA KUNA HANI DA MUMMUNA".
2. Muna samun karin soyayyar Manzon Allah (s.a.w.), ta hanyar karanta mana ayoyin alkar'ani da hadisan ma'aiki daga bakunan malamai daban-daban, wannan kuma yana sa mu kara sanin matsayin Manzon Allah (s.a.w.)
3.  Yaranmu suna tashi da soyayyar Manzon Allah (s.a.w.), domin sanin kowa ne duk wanda ya tarbiyyantu da salatin Annabi yana kore masa dukkan bakin cikin da ke damunsa, ban da lada wanda Allah shi kadai ne ya san yawansa, Allah ka yi dadin  tsira da aminci da jin kai a kan Annabi Muhammadu da alayensa, kamar yadda ka yi akan Annabi Ibrahim, domin kai Hamidun Majidun ne.
Abubuwan da ake samu na falala a wurin maulidi ba za su kirgu ba, kawai in ban da ma lalacewa da ta samu wasu, yaushe ne ma wai har musulmi zai tsaya yana jan ido akan don me za a tuna da ranar haihuwar Manzon Allah (s.a.w.), bayan Manzon Allah da kansa ma ya azumci ranar haihuwarsa.
Imamu Muslim ya fitar a cikin sahihin littafinsa, ya ce: An tambayi Manzon Allah (s.a.w.) dangane da azumin litinin. Sai ya ce: “Saboda wannan ranar aka haife ni” 

Daga cikin dalilansu na haramta ko karhanta maulidi har da: Don me sai ranar haihuwarsa muka ware don yin Maulidi, ai da sai mu rinka yi kowace rana kuma a kowane wata, ba sai watan haihuwarsa ba.
To suma masu irin wannan tunani, sai mu ce da su: Mun ga Manzon Allah  (S.A.W) duk raneku bai dauki kowacce ba, sai ya dauki ranar haihuwarsa. Har aka tambaye shi ya ce: Saboda ranar haihuwarsa ce.
To ka ga ashe mu yin maulidinmu ya dace da watan da aka haife shi (S.A.W), da kuma ranar ya dace da sunnarsa.
Duk da mafi yawan masu haramta maulidi ba wai suna haramtawa ne a kan  hujja ba, a'a, kawai suna haramtawa ne saboda son rai.
Ina kira ga masu cewa maulidi bidi'a ne, kamar yadda bayani ya gabata cewa Salaf ba su yi, to yanzu bisa wadannan hujjoji ta bayyanar masa cewa Salaf sun yi sune ma kan gaba wajen yin maulidi.
Dan uwa mai karatu, kamar yadda ka sani ko na ce ka karanta ma'aunai wajen auna abun da za a ce sunna ne ko bidi'a, su ne littafin Allah (S.W.A.), Sunnar Manzon Allah (s.a.w.), Ijma'in Malamai.
To duk wani abu ko wani ma'auni, wajen wadannan abubuwa uku,  komai kimarsa, in dai bai dogara da dayan wadannan abubuwan ba, to abin yin watse ne da shi. Mai karatu sai ka kalli waccan magana ta masu kokarin haramta maulidi. Manzon Allah (S.A.W) yana cewa “DUK WANDA YA FARI WANI ABU, DA BA YA DAGA CIKIN AL’AMARIMU WANNAN, TO ABIN MAYARWA NE”
Sannan ya sake cewa: 'ABIN DA MA'AIKI YA ZO MUKU DA SHI KU RIKE SHI, ABIN DA YA HANE KU KU HANU'.
((وما آتاكم الرسول فخذوه ومانها كم عنه فانتهوا))[9]
Ya dan uwa mai karatu, ka dubi fadin Allah, duk abin da Manzon Allah (S.A.W) ya zo da shi ku riki wannan abin, abin da ya hane ku to ku hanu, wannan Manzon Allah kenan (S.A.W), masoyin Allah a kan duk halittunsa (S.A.W).
Shin ga wadanda suke da wannan ra’ayin haramcin maulidi, ba su yarda da cewa abin da Manzon Allah (S.A.W) ya halatta halal ne har ranar alkiyama ba, abin da kuma ya haramta haramun ne har ranar alkiyama ba.
((حلال محمد حلال إلى يوم القيامة وحرامه حرام إلى يوم القيامة))
Tambaya ga masu ganin maulidi a matsayin bidi'a, to mun san hadisin da ya yi magana a kan bidi'a. Ya ce ne: "DUKKAN BIDI'A BATA CE, DUKKAN BATA NA KAI MA'ABOCINSA WUTA".
((كل بدعة ضلالة و كل ضلالة فى النار))

            Ko kuwa zabar ranar haihuwar Manzon Allah (S.A.W) ta zama ranar farin ciki ne da yawaita salati ga annabi sama da yadda muke yi a ranar da ba ita ba, da ciyar da abinci ga junanmu da ziyartar 'yan uwanmu da girmama Allah da tsarkake shi da sauran ayyukan alheri su ne suka zama haramun? Wadanda ba su da asali a addini?
  Sannan yin maulidi yana cikin wane gida ne daga cikin wadannan gidaje guda biyu: Bidi'a mummuna? Bidi'a Kyakkyawa?
Idan kana cikin masu ganin maulidi a matsayin mummunar bidi'a ne, to sai na ce maka ka 'yanta kanka ka koma makaranta. 'Yanta kanka da na ce ka yi shi ne ka gane ka san gaskiya sannan ka san mai gaskiya. Ba a sanin gaskiya da mazaje, domin kuwa in dai mutum ba Annabi ba ne, kuma ba Ma'asumi ba ne shari’a ba ta yarda da wannan mutumin ya zama shi ne madubinka na gane gaskiya ba, ta yadda za ka ce ai tun da ka ga malam wane ko Ustaz wane yana yin kaza ai gaskiya ne.
Ko kuma tun da ka ga Malam wane ba ya yi duk iliminsa, ga shi a fuska dai mai tsoron Allah ne, ga shi kuma da bincike amma ba ya yi kawai ya ishe ka hujja ya zama wannan abin ba gaskiya ba ne?
Sai na ce da kai: ka zama bawan wani a tunani, ko da ka sani ko ba ka sani ba.










YANKA RAGON SUNA
Jalaluddin Suyudi ya kawo a cikin littafinsa mai suna Alhawi Lil Fatawa, shafi (197) mujalladi na daya. Ya ce: "Lallai ta bayyana daga cikin hadisai da Baihaki ya ruwaito daga Anas ya ce: “Lallai Manzon Allah (S.A.W.) bayan Allah ya aiko shi, ya yanka wa kansa ragon suna, tare da cewa abu ne sananne lokacin da aka haife shi, kakansa Abdulmudallabi ya yanka masa rago a ranar bakwai da haihuwarsa.
Ya ce: "Hakika ba a yanka wa mutum rago sau biyu". Wannan ya yi nuni da cewa wannan akikar ta biyu da Manzon Allah ya yanka, domin bayyanar da godiyarsa da samar da shi rahama ga al'umma gaba daya, da haifarsa da ciyar da abinci domin neman yardar Allah da bayyanar da farin ciki. Wannan Suyudi ke nan a cikin littafin Alfatawa.
Wannan sanin kowa ne ana yanka ragon suna sau daya ne ga kowa, amma Manzon Allah (S.A.W) ya sake yanka wa bayan Allah ya ba shi kur'ani izuwa al'ummar duniya, domin godiyarsa ga Allah (S.W.T.). To shi a kan kansa ya yi haka, to ina ga mu da ya zo ya shiryar da mu ya ceto duniya daga bakin zalunci da ta samu kanta a ciki, idan ma ba mu yi wani abu na nuna godiya ga Allah ba, lokaci bayan lokaci ai mun zama butulu.
An yi al'umomi kafin mu, domin son da Allah yake yi mana bai yo mu tun wancan lokacin ba, sai ya yo mu cikin al'ummar Manzon Allah (S.A.W) wanda ya fi so a kan duk halittunsa, ya sa mu mune mafi alkhairin al'umma da aka yi daga mutane.
((كنتم خير أمة أخرجت للناس)) [10]
Don haka yin Maulidin Manzon Allah sunna ne, ina wadanda suke cewa Manzon Allah bai yi ba? Sahabbai ba su yi ba? Salaf ba su yi ba? Sai a koma makaranta!
Duk da ba abin mamaki ba ne ya zama wani ya karanta amma bai fahimta ba, saboda akwai wadanda suke karatu amma ba suna yi ba ne da basira, a'a, ga shi fa sun karanta ko an karanta musu, amma su ba su da 'yancin su fahimta, sai dai wani ya dora su akan fahimtar da yake ganin ita ce fahimta mai kyau.
To irin masu wannan yanayin ko da sun karanta ko ka yi musu bayani sai ka ji sun ce: Sai na tambayi wane, ko sai na tambayi malam wane!
Ka ga mai irin wannan yanayin ya wulakantar da baiwar da Allah ya yi masa ta hankali da tunani da ilimi. Ko kuwa ka ji ya ce: "Haba da a ce abin da na karanta ko na ji din nan gaskiya ne, ai da malam wane ya aikata, saboda shi a wurinsa malam wane shi ne ma'aunin gaskiya, duk abin da ya ce gaskiya ne to shi ne gaskiya, abin da kuma ya ce ba gaskiya ba ne, komai bayyanar gaskiyar abin da hujjoji to ba gaskiya ba ne!
Bayani ya gabata cewa, ba a gane gaskiya ta irin wannan hanyar.
Sayyidina Ali dan Abi dalibi (k.w.) yana cewa: “KADA KA ZAMA BAWAN WANINKA, ALHALI ALLAH YA HALICCE KA DA.”
((لا تكن عبد غيرك وقد خلقك الله حرا))
Manzo (S.A.W) ya ce: "NA RANTSE DA WANDA RAINA KE KARKASHIN IKONSA, DAYANKU BA ZAI ZAMA MAI IMANI BA, HAR SAI YA FI SONA FIYE DA YADDA YAKE SON MAHAIFINSA DA 'YA'YANSA DA SAURAN MUTANE".
((والذىنفسى بيده لايؤمن أحدكم حتى أكون أحب الناس إليه من والده وولده وسائر الناس))

A wani hadisin ya kara da cewa (S.A.W) “DAYANKU BA ZAI YI IMANI BA, HAR SAI NA KASANCE NI NA FI SOYUWA A GARE SHI, FIYE DA ‘YA’YANSA DA MUTANE GABA DAYA.
((لا يؤمن أحدكم حتى أكون أحب إليه من ولده والناس أجمعين))

Soyayya wata dabi'a ce da ba ta boyuwa ga ma'abocinta, sai dai in bai sami damar da zai bayyanar da ita ba, to tunda ya zama sharadai na cikar imani, dole sai mutum ya so Manzon Allah (S.A.W) fiye da yadda yake son kansa da iyayensa da 'ya'yansa da sauran mutane gaba daya.
To mece ce soyayya?







SOYAYYAR MANZO (S.A.W) A CIKIN LITTAFIN ALLAH (S.W.T)
Allah madaukakin Sarki yana fada a cikin alkur’ani mai girma, yana cewa da muminai: KA CE In ya kasance iyayenku da ‘ya’yanku da ‘yan uwanku da matanku da danginku da dukiyoyinku da ku ka tara, da kasuwancinku, ku ke jin tsoron lalacewarsa da gidaje wadanda ku ka mallaka suka Fi soyuwa a gare ku, sama da Allah da Manzonsa, da jihadi a tafarkin Allah, to ku saurara har Allah ya zo da al’amarinsa (Azabarsa).
KUL IN KANA ABA’UKUM WA ABNA’UKUM WA’IKHWANUKUM WA AZWAJUKUM WA ASHIRATUKUM WA AMWALUN IKTARAFTUMUHA WA TUJARATUN TAKHSHAUNA KASADAHA WA MASAKINA TARDAUNAHA AHABBA ILAIKUM MINALLAHI WA RASULIHI WA JIHADIN FI SABILIHI FATARABBASU HATTA YA’ATIYAl LAHU BI AMRIHI INNAL LAHAS LA YAHDIL KAUMAL FASIKIN.

)قل إن كان آبائكم وأبنائكم وإخوانكم وعشيرتكم وأزواجكم وأموال إقترفتموها وتجارة تخشون كسادها ومساكن ترضونها أحب إليكم من الله ورسوله وجهاد في سبيله فتربصوا حتى يأتي الله بأمره إن الله لا يهدي القوم الفـسقين). [11]
Suratut Tauba , aya ta 23.
Wannan ayar da na kawo ita ce ta mayar da soyayyar Manzon Allah ya zama dole, in dai kai mumini ne dole ka so Manzon Allah (S.A.W) sama da yadda ka ke son wadancan abubuwan da ayar ta zo da su guda takwas.
Allah gwanin hikima, idan ka duba abubuwan da Allah ya jero za ka ga su suka fi komai a wajen duk wani mutum, amma Allah ya sanya su dole sai ka fi son Manzonsa (S.A.W) sama da yadda ka ke son su.

SOYAYYAR MANZON ALLAH A CIKIN HADISI

(1) Manzon (S.A.W) ya ce: ‘Dayanku ba zai yi imani ba, har sai ya kasance ni na fi soyuwa a gare shi daga dansa da sauran mutane gaba daya.’

‘LA YUMINU AHADUKUM HATTA A KUNA AHABBA ILAIHI MIN WULDIHI WAN NASI AJAMA’INA.’

(لا يومن أحدكم حتى أكون أحب إليه من ولده والناس أجمعين).

 (2) Manzo (S.A.W) ya ce: ‘Na rantse da wanda raina yake karkashin ikonsa, dayanku ba zai yi imani ba, har sai na kasance ni na fi soyuwa a gare shi sama da mahaifinsa da ‘ya’yansa.’
“WALLAZI NAFSI BIYADIHI, LA YUMINU AHADUKUM HATTA AKUNA AHABBAN NASI ILAIHI MIN WALIDIHI WA WULDIHI”.

(والدي نفسي بيده لا يومن أحدكم حتى أكون أحب الناس إليه من والده وولده).

 (3) Manzo (S.A.W) ya ce: ‘Na rantse da Allah dayanku ba zai zama mumini ba har sai na kasance mafi soyuwa a gare shi sama mahaifinsa da ‘ya’yansa.
“WALLAHI LA YAKUNU AHADUKUM MU’UMINAN HATTA A KUNA A HABBA ILAIHI MIN WALADIHI WA WALIDIHI”
(والله لا يكون أحدكم مؤمنا حتى أكون أحب إليه من ولده ووالده).

 (4) Manzo (S.A.W) ya ce: ‘Dayanku ba za ya yi imani ba har sai na kasance mafi soyuwa a wajensa fiye da yadda yake son kansa.’
LA YUMINU AHADUKUM HATTA A KUNA AHABBA ILAIHI MIN NAFSIHI.

(لا يؤمن أحدكم حتى أكون أحب إليه من نفسه).

(5) An karbo daga Anas dan Maliku (r.a), ‘Lallai wani mutum ya tambayi Manzo (S.A.W) cewa, yaushe ne ranar tashin alkiyama? Sai Manzo (S.A.W) ya ce da shi: ‘Me ka tanadar wa wannan ranar ta tashin alkiyma?
Sai mai tambayar ya ce: ‘Ban tanadi komi ba, sai dai ni ina son Allah da Manzonsa.’ Sai Manzo ya ce: ‘Kana tare da wanda ka ke so.’
Sai Anas (r.a) ya ce: ‘Ban taba yin farin ciki da wani abu ba kamar yadda na yi farin ciki da fadin Manzon Allah (S.A.W)  “Kai kana tare da wanda kake so”.
AN ANAS ANNA RAJULAN SA’ALAN NABIYA (S.A.W), ANIS SA’ATI FA KALA MATAS SA’ATU, KALA WAMA A’ADATTA LAHA? KALA: LA SHAI’A ILLA ANNI UHIBBULLAHA WA RASULAHU. FA KALA: ANTA MA’A MAN AHBABTA”.
KALA ANAS:  FAMA FARIHNA BI SHAI’IN FARAHINA BI KAULIN NABIYI (S.A.W): ANTA MA’A MAN AHBABTA”.

)عن أنس أن رجلا سأل النبي صلى الله عليه وآله وسلم عن الساعة, فقال: متى الساعة؟ قال وما أعددت لها؟ قال: لاشئ إلا أني أحب الله ورسوله. فقال: أنت مع من أحببت. قال أنس: فما فرحنا بشئ فرحنا بقول النبي (ص): أنت مع من أحببت).

(6)  Manzo (S.A.W) ya ce; ‘Wadanda na fi tsananin soyuwa a gare su, cikin al’ummata, sune wadand za su kasance a bayana,  dayansu zai so ya rabu da iyalinsa da dukiyarsa  domin ya ganni.’

(أشد أمتي لي حبا يوكون بعدي يود أحدهم أنه فقد أهله وماله وإنه رآني).

(7) Lallai wasu mutune a cikin al’ummata za su zo a bayana, dayansu  zai so da ya sayi ganina da ahalinsa da  dukiyarsa.
(إن أناس من أمتي يأتون بعدي يود أحدهم لو اشترى رؤيتي بأهله وماله).
Dan uwa mai karatu, wadannan hadisan da na kawo a kan soyayyar Manzon Allah (S.A.W) idan kana so ka gansu don ka kara nazari, ka san cewa lallai shugaba (S.A.W) duk inda ka kai da sonsa sai dai ka yi iya imaninka kamar yadda ya gabata. Mai yiwuwa mai karatu ya ce ai duk musulmi yana son Manzon Allah (S.A.W).
Sai na ce wannan haka yake. To amma fa yana bayyana a fili ta hanyar aikin da mai son yake yi wa abin soyayyar. Idan kana son ganin wadannan hadisai ka iya komawa zuwa ga wadannan litattafan:
1 – Sahihul Bukhari.
2 - Sahihu Muslim.
3 – Tirmizi.
4 – Nisa’i.
5 – Kanzul Ummal, mujalladi na biyu.
Malamai  sun yi maganganu akan soyayyar Manzo (S.A.W), kamar yadda zan kawo su.
Imamu Kurdabi ya ce: Duk wanda ya yi imani da Annabi, ingantaccen imani ba ya rasa wani abu a zuciyarsa na soyayyarsa, za ka sami wasu sun kai kololuwa wajen soyayyarsu ga Manzon Allah (S.A.W). Ta yadda mutum zai so ya ba da ‘ya’yansa da dukiyarsa saboda ya gan shi.
Za ka sami wasu kuma soyayyarsu ta yi kasa sosai, suma saboda iya saninsu ga Manzon Allah (S.A.W) ke nan. Misali: Kadan daga cikin abubuwan da suka nuna soyayyar  annabawan Allah  ga Allah, saboda saninsa da suka yi fiye da sauran mutane, shi ya sa son yake bayyana a ayyukansu. Mu dauki Annabi Yusuf (A.S) irin jarrabawar da ya shiga a rayuwa, amma kullum soyayyarsa ga Ubangiji sai karuwa ta ranka yi.
Ma’aiki Annabi Nuhu (A.S), mu tawo har zuwa kan Manzon (S.A.W). Don haka duk inda ka ji so, to wannan son ba ya tabbata sai an aikata shi. Wannan aikin kuma shi ne jarrabawa.
Don haka kirana ga al’ummar musulmi shi ne, mu dauki watan maulidinsa (S.A.W) ya zame mana watan da ya fi kowane wata wajen yawaita salati a gare shi, da yawaita sadakoki da ciyarwa da ziyartar ‘yan uwa da abokai da halartar  wa’azozi a kan hadin kanmu, da sanar da yaranmu abin da muka sani dangane da Manzon Allah (S.A.W), domin sanin hakikaninsa (S.A.W) sai dai Ubangijinsa.
Ya kai mai kin jinin maulidi saboda bidi’a ne (a wajenka) ina fatan yanzu ka fahimci cewa maulidin Manzo sunna ne da Manzon Allah(S.A.W) ya aikata ta hanyar yanka abin yanka da yin azumi, saboda murnar ranar haihuwarsa, kuma in dai kana kin maulidi ne saboda kai a wajenka bidi’a ne, kuma ka kasance kana yaki da bidi’a, a lokaci guda kuma kana ganin sallar tarawihi cikin jam’I sunna ce, to sai ka gane yanzu ta bayyanar maka maulidi sunna ne sallar tarawihi bidi’a ce, kamar yadda mai karatu ya karanta a baya, daga sayyadina Umar (r.a), sai ka ga ashe kai kana fada da bidi’a amma ka fi kowa aikata bidi’a ba tare da ka sani ba, kuma kana fada da sunna ba ka sani ba.
A nan za mu iya cewa: Soyayya wata aba ce da ba ta cika  amsa sunanta ba, dole sai an hada ta da biyayya, ta fadin Allah ta'ala: "KA CE IN KUN KASANCE KUNA SON ALLAH KU BI NI".
((قل إن كنتم تحبون الله فالتبعوني)) [12]
To ga shawara ga wanda yake ganin shi a wajensa soyayyar Manzon Allah (S.A.W) ta takaita ne kawai a yin da'awa ba tare da aiki ba, to ya sani akwai wadanda su soyayyar da suke yi wa Manzon Allah(S.A.W), ta fice kawai ya yi da'awar shi Ahlus-sunna ne ya yi shiru, ina abin ya wuce nan, dole ne sai an gani a duk wasu kai kawo nasa.
Idan mai karatu ya dubi hadisin da ya karanta a baya, zai fahimci wannan bayanin idan har dayanmu zai samu dama wata rana ya shirya walima, ya gayyici mutane a taru a ci abinci a yi addu'a a tashi, saboda ya nuna godiyarsa ga Allah da zagayowar ranar haihuwarsa, kuma wannan bai zama haramun ba, to ina ga raya ranar haihuwar Manzon Allah  (S.A.W).
Wannan mutum ba zai taba zama mumini ba har sai ya so Manzon Allah (S.A.W) sama da yadda yake son kansa.
Kai, mai karatu ina fatan ko da a ce ba ka taba jin cewa Manzon Allah ya yi azumi ranar da ta dace da ranar haihuwarsa ba, har aka tambayeshi, ya yi karin bayani da cewa godiya ce ga Allah ta'ala, saboda samar da shi da ya yi. Ko kuma ba a taba jin cewa Manzon Allah (S.A.W) ya yanka abin yanka aka tambaye shi, sai ya ce: Saboda ranar haihuwarsa ce .
A matsayinka na Musulmi mai kaunar Manzon Allah (S.A.W) ai ya kamata ka dauki ranar haihuwarsa a matsayin babbar rana, wacce babu wata rana da ta kai ta kima.
Wannan ko da ba ka dubi abubuwan da suka faru a ranar haihuwarsa ba, saboda kawai samuwarsa ((S.A.W) ni'ima ce da ta fi kowacce ni'imomi da Allah ya yi mana.

SUWAYE  AHLISSUNNA?
 Masu kiran maulidin Manzo (S.A.W) da sunan bidi’a, a lokaci guda kuma sun sa wa kansu Ahlissunna!
Tambaya: Manzo (S.A.W) Ya sa wa wasu suna? ko kuwa ya kira wasu daga cikin sahabbansa da Ahlissunna?
Amsa: Duk masu kiran kansu da sunan Ahlissunna ba sa fadin cewa Manzo (S.A.W) ne ya sa wa wasu gungun sahabbansa sunan Ahlissunna, don haka ka ga ashe tun da farko mai dokar barci ya bige da gyangyadi, tun da mai fada da bidi’a a lokaci guda sai ga shi farkon sunan da ya sa wa kansa da kansa ya fara da bidi’a.
To amma ba zan yi mamaki ba, don haka kai ma mai karatu ka da ka yi mamaki, saboda Allah (S.W.T) ya fada a cikin Alkur’ani mai girma: (Gannai ba sa makancewa, sai dai zuciyoyin da suke cikin kiraza sune suke  makancewa)
Masu hikima suna cewa :
‘Duk wanda ya ce  ni wane  to  ba shi ba ne’

(من قال أنا فليس هو)

“MAN KALA ANA FA LAISA HUWA”
Misali: Kamar mutum ne za ku yi mu’amala da shi ta kasuwanci ko wata mu’amala daban, wacce take bukatar rikon amana. Shi kenan farkon haduwarku da wannan mutum, ku ka gaisa gaisawa ta Musulunci ko ta al’ada, ko ma ba ku ma gaisa ba, sai ku ka shiga maganar da ta hada ku ta (kasuwanci), kai tsaye sai ka ji ya ce da kai ‘Bari na fara gabatar maka da kaina, sai ya ce: ‘Da farko ina so ka san cewa:
1-      Ni mutumin kirki ne.
2-      Na san mutuncin mutane.
3-      Na iya mu’amala da mutane.
4-      Na san yadda zan yi duk harkar da muka kulla, ba za mu fadi ba sai dai mu ci riba.
5-      Ban san wani mutum ba da ya fi ni rikon amana.
6-      Duk abin da na fada maka shi ne daidai.
7-      Duk abin da ba mu yarda da shi ba ba daidai ba ne, saboda mu ne mu ke bin sunna!
8-      Daga karshe bayan ya gama tsara maka wadannan maganganun na matsayinsa, ya ce maka kuma ni malami ne.
To haka fa masu haramta maulidi su ke, babu wanda yake sallah daidai sai su, don haka ma da yawansu ba sa bin kowa sallah sai mai irin tunaninsu ko kuma kai ka bi su, da yanwasu ba sa yin sallah  a  sauran masallati sai masallacinsu, saboda idan sun yi a wani wanda ba nasu ba, suna ganin kamar ba su yi ba, saboda masallatan ‘yan bidi’a ne, musu yin maulidi.
Dan uwa mai karatu, ka ga a matsayinka na mai hankali ko ba a ce maka komai ba, ka san duk wanda ya yi wadancan maganganu, idan ka sake ku ka kulla harka da shi ka san da wanda ka kulla, dole zai zalunce ka, za kuma ka yi asara, zai ci amanarka ko da za ta kai ku ga zuwa gaban shari’a, zai iya rantsewa da wanda ya halicce shi a kan karya, saboda me? saboda sabawar da ya yi wa umarnin Allah (S.W.T) yana cewa: “Ka da ku tsarkake kanku, Allah shi ya fi sanin mai tsoronsa.”
Mai karatu, ka da ka yi mamaki ka ga cewa malam wane  yana haramta maulidi, ka ce ai da maulidi sunna ne da malam wane bai haramta ba, saboda ai malamin cikakken Ahalissunna ne. A’a, matsalar da take faruwa a yau ita ce, wasu malaman sun dauki mutane su ne jarinsu, za ka iya yarda da ni idan na ba ka misali, za ka ga daga cikin masu ganin maulidi bidi’a ne, a yau su suka fi kowa kokarin duk inda suka san jama’a suna haduwa, to za ka ga ko da shago ne sun samu sun mayar da shi masallaci. Ko ka san dalili?
Dalilin shi ne da ka sami masallaci a wurin da jama’a su ke, ko hanyar da jama’a suke yawan hada-hada to za ka tara mutane, in ka tara mutane za ka rinka samun girma da dan abin hasafi. Don haka ko da za ta kai ga rigima tsakaninsa da Musulmi ‘yan uwansa to sai a yi ta yi, ko da za ta kai ga rasa rai ba zai iya hakura ba. Saboda shi zai ga ya ya ga kamfani ya kafa, nan gaba kadan za a rike masa kan saniya ya yi ta tatsar nono a ce wai ya bari? Komai za a yi sai dai a yi, domin ya mayar da masallaci kamfanin samun abin hasafi.
Abin mamaki ko wane mutum mai hankali zai yarda da ni, a kan cewa hadin kai shi ya fi komai a tsakanin musulmi, Allah yana kiranmu da mu zama tsintsiya madaurinki daya. Manzon Allah (S.A.W) yana umartarmu da mu hada kanmu, amma su masu mayar da masallaci shagon kasuwanci, sai su ce to da ku ke cewa a hada kai a fahimci juna, wato kuna nufin ka aikata bidi’a na yi shiru, ka aikata shirka na yi shiru, amma a hakika tuwan su suke karewa ba wai sunna ba, shi ya sa bas a yadda da duk  wata magana ta hadin kan musulmi, kai ka ce  Allah da Manzonsa (S.A.W) kamar cewa suka yi  a  rarraba.
A to! Ga shi kiri-kiri mutum ya fifita maslahar kansa a kan ta addinin musulunci saboda shi ma wata rana a rinke ce masa malam wane, mai yiwuwa ma wata rana sai ka ji shi a gidan rediyo, shi kuma sai ya ji dadi saboda duniya za ta san shi, jama’a za su taru suna sauraronsa. Don haka ne ire-iren wadannan masu kokarin tarwatsa kan al’ummar Manzon Allah (S.A.W) suke hana mabiyansu su je su dauki littafi su karanta in dai ba wanda suka zabar musu ba.
Ko da kuwa kai ne ka je ka yi gaban kanka ka karanta wani abu, idan ka ga masu yi suna da hujja, sai malam wane ya ce ka daina daukar ire-iren wadannan litattafan, saboda kai ba za ka gane gaskiya ba, don haka bari in yi maka bayanin abin da ka gani. Sai ya warware maka ya mayar da kai cikin kangin  bautarsa  a tunani.
فلا تزكوا أنفسكم هو أعلم بمن اتقى) [13]
“FALA TUZAKKU ANFUSAKUM HUWA A’ALAMU BI MANITTAKA”.
Don haka, duk wanda ya zo ya ce maka shi Ahlissunna ne, sai ka tambaye shi  da cewa: Su kuma sauran Musulmi ‘yan Ahlul bidi’a ne? Idan ya amsa maka da eh, ka ga ya tsarkake kansa a nan, ya fada cikin abin da Allah (S.W.T) ya hana muminai aikatawa.
Idan kamu ya ce maka shi ba yana nufin sauran musulmi Ahalul bidi’a ba ne, sai ka tambaye shi: To Ahalul Kufri ne? Ko Ahalul shirki ne? Idan ya amsa da: A’a. To sai ka tambaye shi ya yi maka bayanin me yake nufi, ko kuwa bai san ma’anar kalmar da ya rada wa kansa ba ne wato ta Ahalussunna.
Idan kama ya ce maka, yana nufin waninsa Ahalul bidi’a ne, to sai ka tambaye shi dangane da hadisin da Manzo (S.A.W) yake cewa: ‘Duk wanda ya shaida babu  wani abin bauta sai Allah, kuma ya shaida Annabi Muhammadu (S.A.W) shi ne ya aiko shi, jininsa ya kubuta a gare mu, da mutumcinsa da dukiyarsa, hisabinsa yana wajen Allah’
Mai karatu ka da ka manta cewa a yanzu muna wani lokaci da mafi yawan masu kiran kansu malamai, suke rige-rige wajen kokarin tara mutane, kowa yana so a ce yana da jama’a a karkashinsa saboda dan amfanin duniya da zai samu, don haka duk yadda zai yi ya ga ya tara mutane to fa zai yi, saboda wasu bukatunsa na kashin kansa.
To mai karatu, ka duba mana shi mai kiran kansa Ahlissunna a lokaci guda kuma yana kiran maulidin Manzon Allah (S.A.W) da bidi’a! Saboda idan ya ce da mabiyansa yanzu ya gano maulidi sunna ne, ko kuma ya ce da su ba matsala tun da Manzo (S.A.W) bai ce ka da a yi ba za su ce ya canza, don haka za su watse su bar shi, shi kuma su ne jarinsa. Ai za ka ga shi a fahimtarsa ya dage wandonsa ya kawo shi kwauri.
Mai karatu ka da mu manta da waccan ayar da na kawo maka a baya, ga shi mutum ido kulu-kulu, amma ba ya ganin gaskiya, saboda zuciyarsa ta makance, to in ba haka ba, ka duba da kyau ko akwai hadisin da yake magana a kan dage wando? Za ka ga hadisin bai ce wando ba, hadisin ya yi magana ne a kan ka da ku bar jelar rawaninku ta rinka jan kasa, ka da ku bar mayafin ku ya rinka jan kasa, ka da ku bar  abayarku ta rinka jan kasa.
To ka ga hadisin yana magana akan dukkan  wadannan abubuwa guda uku, a ciki ba a ambaci wando ba, kuma ma duk mai ido ai ya san ba a jan wando sai dai a ce an take shi, in kuwa haka ne to ina aka samo maganar dage wando a kawoshi kwauri a matsayin sunna, babu wani hadisi, ko wata magana ta Salaf.

ABIN LURA A NAN.
(a)                           Shi  wando yana da suna a Larabci, ma’ana a yaren Larabci, kamar yadda wasu abubuwa suke da suna.
(b)                           Ku gane shi mai dage wando, ba ya kawo maganar dage wando a matsayin ijtihadi ba  ne, a’a, ya ce hadisi ne ya ce a dage wando da kalmar wando, amma da a ce mai dage wando ya ce ijtihadi ne wani malaminsa ya yi, ya ce shi ya fahimta daga wadancan abubuwan da hadisin Manzo (S.A.W) da sunan ka da a ja su a kasa, sai shi kuma ya kara da wando, to ka ga da abin ya zo da sauki, saboda ai dama mujtahidi wajen yin ijtihadinsa zai iya kuskure, saboda ba ma’asumi ba ne.
To ka ga da ko cewa ya yi a saka gajeren wando, kamar ni da ire-iren dalibai sai mu yi shiru mu bar shi da malamai ‘yan uwansa su tattauna, to amma sai bai ce fatawa ba ce wani malami ya bayar ba, kai tsaye sai ya ce hadisi ne, kuma idan ka ce ya kawo maka hadisin, sai ya kawo maka wancan haisin da ya gabata, alhali a cikinsa ba a ambaci wando ba.
Mai karatu, da wannan za ka fara fahimtar misalin da na ba ka a baya, na wannan mutumin da ya ce maka shi mai rikon amana ne, kasan yadda abin yake aikin mutum shi ne yake nuna mutum, ba furuci kawai ba. Ayoyin Alkur’ani da suke magana a kan muminai su so junansu, sannan hadisan Manzon Allah (S.A.W) da suke magana a kan mu so junanmu, sannan akwai hadisan Manzo  (S.A.W) da yawa da  suke magana a kan cewa musulmi dan uwan musulmi ne, sannan kuma ana karanta su dare da rana, amma duk da haka a yau me ke faruwa tsakanin musulmi, kai da ka fara al’amuranka da bidi’a ka ce ba za ka bi ni sallah ba, sai dai ni na bi ka, ka ce masallacin da nake yin sallah bai yi maka ba sai ka yi naka, ka ce mini mai bautar Waliyyai kai ne mai bautar Allah, ka ce mini mushriki kai ne mai kadaita Allah, to tamabaya duk wadannan abubuwan da ka ke fada a kaina duk shi ma sunna ce, kuma sunnar dan Abdullahi (S.A.W)?
Kai! Bari, ba dai sunnar Manzo  (S.A.W). A nan su waye aikinsu ya nuna sune Ahlissunna? Masu son hada kan musulmi ko masu rarraba kan musulm, ta hanyar ware masallatansu? Wadanda aikinsu ya nuna su ne Ahlissunnar Manzo (S.A.W), su ne wadanda ta bayayyana a  aikace.
Allah (S.W.T) yana cewa a cikin Alkur’ani mai girma, yana fada wa Manzonsa (S.A.W):  mafi soyuwar dukkan halittunsa (S.A.W), (Ka yi kira izuwa tafarkin Ubangijinka da hikima da wa’azi mai kyau.) Ma’ana da kalmomi masu kyawu.
‘UD’U ILA SABILI RABBIKA BILHIKMATI WALMAU’IZTUL HASANATI’

) أدع إلى سبيل ربك بالحكمة والموعظة الحسنة)[14]

MAI SON HADIN KAN MUSULMI SHI NE AHLISSUNNA.
Wannan fa ita ce koyarwar Allah ta hanyar  Manzonsa (S.A.W). Kuma Manzo (S.A.W) ya isar. An tambayi ummul miminina A’isha (r.a) dabi’un Manzon Allah (S.A.W), sai ta ce: “Dabi’unsa shi ne Alkur’ani.” Ma’ana, duk abin da Alkur’ani ya ce a yi shi yake yi, duk abin da Alkur’ani ya ce a bari ba za ka taba ji ya aikata ba.
Mai karatu, dubi wannan al’amari, hatta wadanda ba su musulunta ba ga yadda Allah ya ce Manzo ya yi kiransu, to ina ga Musulmi masu shaidawa da LA’ILAHA ILLALLAHU MUHAMMAD RASULULLAHI (S.A.W) kana fada mini munanan kalmomi, da haka ne zan  bar abin da nake yi na yi naka ? Ko kai ba ruwanka da umarnin Allah da Manzonsa da suka fada dangane da ayoyin Allah da hadisan Manzo (S.A.W).
Allah a cikin Alkur’ani yana cewa da Manzo (S.A.W): (Da ka kasance mai yawan fushi, mai kakkausar zuciya da sun tarwatse daga gare ka.
‘LAU KUNTA FAZZAN GALIZAL KALBI LAN FADDUU MIN HAULIKA’.

(لو كنت فظا غليظ القلب لانفضوا من حولك)[15]
To ga shi, kai kuma maganganun da ka ke yi ba  tausasawa, to ta ya ya za ka iya jawo hankalin wani ya zuwa abin da ka ke yi, ko dai kana son rarraba kan al’ummar Manzo ne (S.A.W), ga shi dai duk da imanin da sahabbai su ke da shi, amma Allah ya ce da Manzo (S.A.W) ya kausasa musu harshe da sun bar shi, to ina ga mu. Ta ya ya za ka iya kiran mutane ga abin da ka ke kai ta hanyar kausasa musu harshe?
Dan uwa mai karatu, ka dubi wannan al’amarin da idon basira sosai, ka da kai ma, ka kasance daga cikin wadanda, kullum burinsu shi ne su kawo rarrabuwan kawunan Musulmi, amma a lokaci guda suna ganin wai sunna suke bi, Allah ka kare mu, ka saka mu cikin masu kokarin hada kan Musulmi a duk inda muka samu kawunanmu.





ABIN MAMAKI (1)
Abin mamaki ba ya karewa ga duk wanda yake kallon raya ranar da aka haifi Manzon Allah (S.A.W) a matsayin bidi’a!
Duk da masu wannan magana ta maulidi bidi’a ne, kamar yadda mai karatu ya karanta, sun saka wa kansu suna wanda shi kansa sunan bidi’a ne, kuma wai a matsayin masu yaki da bidi’a. kamar yadda mai karatu ya karanta ko zai karanta, ko ya ji an  ce Manzon Allah (S.A.W) ya yi azumi ranar litinin, sai aka tambaye shi me ya sa ya yi azumi ranar litinin, sai ya ce saboda ranar aka haife shi. Ka da mai karatu ya ce ai ba litinin kawai Manzo (S.A.W) yake yin azumi ba, sai na ce maka haka ne, to amma yanzu muna magana ne game da ranar haihuwarsa, da ya yi godiya ga Allah (S.W.T).
To ka ga ko wannan kadai ya isa ga masoyin Manzon Allah  (S.A.W) ya raya ranar da aka haifi (S.A.W), kai ba ma haka ba, kamar yadda ka karanta Manzo (S.A.W) ya yanka abin yanka, sai aka tambaye shi saboda me? Sai ya ce saboda murnar zagayowar ranar da aka haife shi. Wannan ba maulidi ba ne? Kuma wannan ba nuna murna da farin ciki ba ne?
To ina so kai mai sukar maulidi ka kawo wa masu yin maulidi aya daya, ko hadisi daya, komi rauninsa wanda Manzo (S.A.W) ya ce ka kira kanka Ahlissunna, sauran musulmi kuwa ‘yan bidi’a? ko ka kawo hadisin da Manzo ya kawo kalmar wando kuma ya ce a dage shi.
Ka kawo mini hadisin da Manzon Allah  (S.A.W)ya ce: duk inda ka sami kanka a cikin musulmi ka yi kokari ka ware masallacinka. Ka kawo mini hadisin da Manzon Allah  (S.A.W) ya ce ka shirya gasar musabakar Alkur’ani mai girma, har ya zama akwai ta jiha-jiha, akwai ta kananan hukumomi, akwai ta kasa baki daya akwai ta duniya.
Duk wannan misalan da na kawo suna yi kuma ba sa jin komai, kai har suna jin ma su sunna suke aikatawa. Mai yiwuwa mai karatu ya ce su ma ba su ce sunna suke aikatawa ba, to bidi’a suke aikatawa?!
  Idan mai haramta maulidi zai ce ai akwai hadisi, duk wanda ya assasa wata sunna har zuwa karshen hadisin kamar yadda bayani ya gabata. Sai na ce da shi: Ai Manzon Allah (S.A.W) ya yi maulidinsa kamar yadda ka karanta, ya yanka abin yanka  kamar yadda ka karanta, saboda ranar haihuwarsa. Me ya sa kai ka ke kin yin hakan? Kai har ma kana ganin masu yin hakan a matsayin ‘yan bidi’a.
Mai karatu, ka ga matsalar mutum ya tsarkake kansa da kansa ke nan, ta hanyar nuna shi malami ne ko kuma shi ne yake tare da gaskiya, alhali ba haka ba ne.
A to! Don me ba zan ce haka ba ne? Tun da  ga shi har mutum zai iya shiga gidan rediyo ko kuma ya tara mutane da sunan yana yi musu wa’azi da sunansa na malami, yana ce musu sunnar  Manzo (S.A.W) bidi’a ce. Muna neman tsari da wannan kalma mummuma!
Ga shi Manzo (S.A.W) ya yi aiki, amma saboda malamin ya  tumbatsa ya zo yana kiran mutane al’ummar Manzon Allah (S.A.W) da su kaurace wa wannan aikin. To ka ga ko dai wannan hamshakin malami bai san wancan hadisin ba ne, har yake cewa maulidi bidi’a ne, ko kuwa don shi a dabi’arsa ba ya gane gaskiya ta hanyar da ya kamata ya gane? Hanyar kuwa ita ce: Ka san gaskiya sai ka san mai gaskiya.
To watakila  hamshakin malamin yana da wasu wadanda ya a jiye a matsayin madubin gaskiya, duk abin da suka yarda da shi shi ne mai kyau, kuma shi ne gaskiya. A to, in ba haka ba  in dai har yana bin sunna ne, kuma yana kallon abubuwa da idanuwa biyu, ya ya a lokacin da shi wannan malamin da ya sa wa kansa suna, ya rada wa kansa Ahlissunna zai bijire wa maganar da sayyadina Umar dan Khaddabi (r.a) ya yi.
Ya kira a bin sunna, wanda a lokaci guda Umar (r.a.) ya kira shi  da bidi’a, kamar yadda mai karatu zai gani, mai karatu za ka yarda da ni babu kokwanto lallai sayyadina Umar (r.a) ya fi dukkan wadannan masu kiran kansu ahlissunna a yanzu sanin sunnar Annabi (S.A.W).
Amma mai karatu ko da bai karanta ba, mai yiwuwa ba zai rasa jin an ce  Manzon Allah (S.A.W) ya hana sallar Asham a jam’I, mai karatu mai yiwuwa wane ya ce: To ai  da ya  hana, daga baya  Khalifa na biyu Umar (r.a) ya  sa a yi. kuma duk abin da daya daga cikin Khalifofin nan hudu ya yi daidai ne.
Saboda hadisin da Manzon Allah (S.A.W) ya ce:  Ina horonku da sunnata da sunar Khalifofina a bayana. ku yi riko da ita (sunna) da karfi.”
Koma dai me za a ce ana magana ne akan bidi’a. kuma  dole mu ba wa kanmu  mafita a kan wadanan maganganun.
1-                           Manzon Allah (S.A.W) da ya  yi maganar bidi’a, cewa ya yi dukkan bidi’a  bata ce, kuma dukkanin bata tana kai ma’abotansa cikin wuta.
2-                           Idan ka ce to, ai Khalifa na biyu Sayyadina Umar dan Khaddabi (r.a) shi ne ya assasa ta. Sai na ce da kai shi ma da ya  assasa ta, bai ce mata (tarawihi) sunna ba. kai shi ma ya kira ta bidi ce. Har ma ya ce wanda ya yi barci bai yi ba, ya fi wanda ya yi. Sahihul Bukhari babin da ke Magana a kan sallar tarawihi.
3-                           Ba ka fi sayyadina Umar sanin sunnar Manzon Allah (S.A.W) ba, ta yadda ya kira tarawihi da (bidi’a), kai kuma yau za ka ce sunna ce, ashe ka ga a nan sai mu koma mu kalli Ilmul Usulul Fikihi, mu ga mece ce kowacce ka’ida suka ajiye wajen haramta abu ko halasta shi.
Magana dai ita ce a ka’ida ta Usul ana duban me shari’a ta ce a kan abu, misali shin me Manzon Allah (S.A.W) ya ce a kan abu?
Abin lura shi ne, Allah madaukakin sarki ya ce: Abin da Manzo ya zo muku da shi ku rike shi, abin kuma da ya hane ku ku hanu, ku bar shi.
Don haka idan muka koma ka’ida abin dubawa shi ne , abin da Manzo (S.A.W) ya ce ku yi to dole ku yi, abin kuma da ya ce ku bari dole ku bari. Wanda yana da hadari ke nan mutum ya aikata abin da Manzon Allah (S.A.W) ya hana, yin haka zai kai mutum ga fadawa fishin Allah (S.W.T), Allah ya kare mu amin.
4. Tun da yanzu mun ji cewa yana daga cikin sabuban haramci sai Manzo(S.A.W) ya hana abu sannan yin wani abu ya zama haramun, to mu tunda  bai  ce kada  mu yi mauludi  ba,  ta kowace fuska, to ka ga ashe  yin maulidin Manzon Allah (S.A.W) ba laife bane takowacce irin fuska, sannan   ya fi mai yin sallar tawawihi a jam’i hujja a shari’a, domin ita manzo (S.A.W) ya hana karara, kamar yadda bayani ya gaba ta.
Karin dalili akan haka shi ne:
5. Hadisin da ya zo daga  Manzon Allah (S.A.W), wanda Imamu Muslim ya fitar da shi, a cikin littafinsa Sahihu Muslim, wanda Manzo (S.A.W) yake cewa: Duk wanda ya sunnanta wata sunna (ya assasa) mai kyau, yana da ladan wannan sunnar, da ladan wanda ya yi aiki da ita.
Haka duk wanda ya aikata wata sunnan (ya assasa) mummuna, yana da zunubin wannan sunnar da kuma zunubin wanda ya yi aiki da ita, shi ma ba tare da ya ragi zunubinsa da komai ba.
Dogaro da wannan ingantaccen hadisin, Maulidi sunna ce da fadin Manzon Allah (S.A.W), saboda sunna ce mai kyau kamar yadda  za ka karanta a nan gaba.
Mai karatu sai ka duba a sallar tarawihi a jam’I, a kwai hadisin da yake cewa: Annabi ya hana, sannan sayyadina Umar (r.a) ya kira ta da bidi’a. Amma abin mamaki wanda ya fi kowa tayar da jijiyar wuya, a kan don me ake yin maulidin Annabi (S.A.W), duk da bayanan da suka gabata sai ga shi, shi ne ya fi kowa rawar jiki a kan a yi sallar tarawihi a jam’I, a matsayin wai sunna ce, wanda na san mai karatu zai yarda da ni duk wani malami da zai tara jama’a yana yi musu bayani a kan sunna bai kai daya bisa miliyan ba in za ka kwatanta shi da Umar dan Khaddabi (r.a).
Duk da matsayinsa da saninsa da fahimtarsa da addini, da kiyayewarsa da yin abin da yake ganin shi ne ya dace ya kira tarawihi da bidi’a. To waye a yau zai zo ya ce mana sunna ce mu yarda, ai ko da za mu yarda sunna ce to sai ya kawo mana hujjar da ta fi tamu da muka samu daga Umar dan Khaddabi (r.a). Hujjar za ta iya kasancewa mai yiwuwa sai a amsa wadannan tambayoyin kafin ya iya daukar hanyar da zai gamsar da mai karatu.
Misali:
(a)                            Dole wanda zai yi mana bayani a kan sallar tarawihi a jam’i sunna ce, kuma mu gamsu ko ya gamsar da  mu ya zama ya fi Umar (r.a) sanin sunna.
(b)                            Ko ya zama ya fi Umar (r.a) tsoron Allah da gane hukunce-hukuncen Allah, ta yadda shi ya ce bidi’a ce, shi kuma ya ce sunna ce (tarawihi).
(c)                            Ko kuma ya kasance ya fi shi sanin Larabci duk da shi (r.a) yarensa ne!
To idan har mai cewa maulidi bidi’a ne, sallar tarawihi sunna ce, ba zai iya bamu  ‘yan dalilai ba kamar wadannan daga (a) zuwa (c) ba, to ya sani ba zai  gamsar da mu ba, ta yadda maulidin Annabi ko kebe ranar haihuwarsa a raya ta  ya zama bidi’a. To mai karatu a nan ka ji maganar da sayyidina Umar (r.a) ya yi a kan tarawihi.
Bari na kara maka da dan wani abin mamaki, shi a kan kansa (r.a) bai taba yin tarawihi  a jam’I ba. wannan kuwa ko da ba ka karanta ba ya ishe ka dalili. Sayyadina Umar (r.a) ba zai aikata bidi’a ba komi kankantarta, in da kuwa ya yi  to da bai kira ta bidi’a ba kansa. Don haka mai karatu a matsayinka na mai hankali, ya kamata ka tambayi kanka, wai mene ne dalilin da ya sa wasu ‘yan tsirari daga cikin Musulmi, idan watan haihuwar Annabi (S.A.W) ya kama suke samun kansu cikin kunci da damuwa, kawai saboda al’ummar Musulmi suna murna da zagayowar watan da aka haifi  Annabi Muhammadu (S.A.W), har ta kai wasu ba sa iya  barin iyalansu su yi sabon dinki su saka a cikin watan, kawai wai saboda ka da  a ce sun yi haka ne saboda maulidi. Mene ne ya yi zafi haka?
Ina so mai karatu ya koma da tunaninsa baya kadan, a kan hadisin da yake magana a kan  duk wanda ya assasa sunna mai kyau ko mara kyau, me Manzo (S.A.W) ya ce akansa? Sai ka ba wa kanka amsa, idan har maulidin shugabammu (S.A.W) yana cikin sunna mai kyau saboda abubuwan da ake gabatarwa, kamar  karatun Alkur’ani mai girma, karanta tarihin rayuwar Annabi (S.A.W) da ta Ahalin gidansa da Sahabbansa masu girma.
Da a ce sallar tarawihi a jam’I ba bidi’a ba ce, ko kuma a ce Manzo  (S.A.W) ne ya ce a yi, kuma bai ce a dai na yinta a jam’I ba, ko Manzo  (S.A.W) ya ga ana yi bai hana ba, da ba zai taba yiwuwa ba sayyadina Umar Khalifa. Na biyu duk soyayyarsa da Manzo da bin sunnar Manzon, amma ya kira ta da bidi’a. kai ai ko da wani ne ya kira ta da bidi’ a da ya tsawatar masa.
Balle shi da kansa ya kira ta da bidi’a kamar yadda ya ce: “Madalla da wannan bidi’a (sallar Tarawihi a jam’i). Wanda ya yi barci ya fi wanda ya yi ta.’ 
Mai karatu wannan hadisi da Bukhari ya ruwaito haka yake, amma an yi kokarin a ce yana nufin (r.a) wanda ya yi barci ya fi wanda ya yi ta, wai yana nufin sai tsakar dare ya tashi ya yi ta, shi ma ba ana nufin a yi ta a jam’i ba, a’a mutum ya yi a gidansa shi kadai (shi mai sallar). To ko ma dai meye shi (r.a) abin da ya ce ke nan kuma ya kira ta da bidi’a
Abin mamaki a nan, bai wuce duk watan Ramadan idan ya tsaya mu rinka yin sallar tarawihi a jam’i ba, duk da waccan maganar ta Umar (r.a) wancan malamin yana ta karfafa mu da mu yi waccar bidi’ar, mai yiwuwa ma shi ne zai yi mana ko yake mana limanci ko waninsa, wanda shi ma shi ya rada wa kansa suna (Ahlisussunna).
Amma da watan Rabi’il Auwal, watan da aka haifi Manzo (S.A.W) ya kam, sai ka ji yana cewa a yi hattara da ‘yan bidi’a masu karyar son Manzon Allah. (S.A.W) Maulidin Annabi haramun ne, saboda bidi’a ne.
Abin mamaki ba ya karewa mai karatu, shi fa wannan mai cewa ka da a yi maulidin Annabi (S.A.W) bai
Kawo ayar da Allah ya ce ka da a yi maulidin Annabi ba, kuma bai kawo hadisin da Manzo (S.A.W) ya ce ka da a yi maulidina ba, komai raunin hadisin. Bai kawo hadisi daga wani sahabin Annabi ba, wanda ya ce ka da a yi maulidin, ko da kuwa sahabin ba shi daga cikin Khulafa’ur rashidin, amma ga shi na biyu daga cikin Khulafa’ur  rashidina ya ce sallar tarawihi a jam’i bidi’a ce, amma sun fi kowa kwadaitarwa kan yinta har da mata.
Bugu da kari, da a ce sallar tarawihi Manzo (S.A.W) ya yi kuma bai hana a yi a cikin jam’I ba da mun ga sayyadina Abubakar (r.a) ya yi ta a jam’i, domin a da’awar (wadannan masu kiran Kansu ahlissunna) sun fi kowa son aikata abin da yake sunna ne.
Kamar  yadda mai karatu ka karanta a baya, na ce babu hadisi komai rauninsa da ya ce Manzo (S.A.W) ya ce ka da a yi maulidi balle aya daga alkur’ani mai girma. Ya dan uwana  mai karatu, ina so na tunatar da kai yin wani abu ko barinsa a shari’a shi ne abin da Manzo (S.A.W) ya zo muna da shi, ka yi wanda ya hada da abin da ya aikata da wanda ya yi umarni a aikata da kuma wanda aka aikata a gabansa bai hana ba, ko kuma aka aikata ya tabbatar da shi, abin kuma da ya hana mu hanu mu bar shi komai son da muke wa abin.
Don haka ba shi daga ma’auni ka ce abin da Manzo  (S.A.W) bai yi ba wannan abin ya zama haramun. To in har haka ne ya ya abin da Manzo (S.A.W) ya aikata zai zama haramun, sannan abin da ya ce a bari ya zama sunna, alhali Allah (S.W.T) ya fada a cikin alkur’ani: Abin da Manzo  (S.A.W)ya zo muku da shi ku rike shi, abin kuma da ya hane ku ku hanu.

(ما اتى كم الرسول فخذوه وما نهاكم عنه فانتهوا)[16]

“MA ATAKUMUR RASULU FA KHUZUHU WAMA NAHAKUM ANHU FANTAHU”.
 Ya zo a cikin hadisin da Bukhari ya fitar ya ce: Manzo (S.A.W) ya ce: ‘Ku yi sallah a dakunanku, saboda lallai mafificiyar sallar mutum, ita ce wadda ya yi a dakinsa, sai dai sallar wajibi.’ Za ka iya samun wannan hadisi a littafin Sahihul bukhari, mulalladi na biyu shafi na (214). Ko a Sahihu Muslum na daya (039). Ko kuma Tirmizi na daya (279).

(صلوا في بيوتكم فإن أفضل صلاة المرء في بيته إلا المكتوبة).
“SALLU FI BIYUTIKUM FA’INNA AFDALA SALATIL MAR’I FI BAITIHI ILLAL MAKTUBATI”
A nan zan tsaya da ‘yan misalan da na kawo a yanzu, wanda yanzu ta bayyanar wa mai karatun maulidin Manzon Allah (S.A.W) sunnar Manzo ne (S.A.W). don haka mu masoya Manzon Allah (S.A.W) muna ganin raya waccan sunna ta maulidi na daga cikin abubuwan da wannan addini na musulunci yake daukaka da  raya su, wannan sunna ta Manzon Allah (S.A.W) ana aiki da ita a duk inda musulmi su ke a cikin wannan duniya,  kasashe  daban-daban da garuruwa daban-daban na musulmi.
Sai dai kamar yadda ka sani mai karatu, soyayyar Manzo (S.A.W) mataki-mataki ce, ma’ana matsayi-matsayi ce, don haka za ka ga inda kai kana gani ka yi iya abin da ka yi, sai ka ga wani ya zarce ka kuma haka al’amarin yake, tun lokacin Manzo (S.A.W), ko a cikin sahabbai za ka sami cewa wane ya fi wane.
To ka ga ko a nan katsaya ka nutsu, mai karatu za ka iya fahimtar wasu abubuwa har ka yi tambaya kamar haka:
1 – Me ya sa mai haramta maulidi duk da babu wani hadisin da yake kawowa, wanda ya ce kada a yi yake tsanantawa da lallai sai an daina maulidi? Saboda shi a iya iliminsa ko iya ilimin wanda yake bi a wurinsa bidi’a ne.
2 – Me ya sa yake kwadaitarwa da duk iya abin da yake da shi na baki da zai yi wa mutane bayani ko na kudi da zai biya a buga a jaridu ko kuma a yada a gidajen radio domin mutane su yi sallar tarawihi, duk da sayyadina Umar (R.A) dan Khddabi ya kira tad a bidi’a.
3 – Shin an samu hadisin daga wani sashin ko da kuwa mai rauni ne, wanda ya ce maulidin shugaba (S.A.W) bidi’a ne? kamar yadda aka samo daga sayyadina Umar da ya kira sallar tarawihi da bidi’a?
4 – Ko mai cewa a yi sallar asham ya fiduk sauran musulmi sanin maganar sayyadina Umar (R.A) da zai zo ya ce haka yake nufi ko ba haka yake nufi ba?
5 – Don me mai haramta maulidi ba zai dubi waccanr ka’ida bat a duk abin da Manzo ya zo muku da shi ku rike shi, kuma abin da ya hane ku ku bar shi?
Mai karatu akwai tambayoyi da yawa da duk mai hankali ba zai rasa sub a, saboda yadda mai haramta yin  maulidi yake nuna bacin ransa idan watan maulidin Manzo (S.A.W) ya kama, sai ka ga mene ne ya yi zafi haka duk daga abubuwa da yawa, wadanda suke  suna jawo raba kan musulmi, amma wannan ba shi ne ya dame shi ba, aikinsa zai nuna maka kamar ma haka yake so, saboda duk lokacin da ka ce da shi a hada kai zai ce maka kana so a hada kunu da zawayi ? Yana nufin shi ne kunu sauran Muslmi zawayi. Kuma wnanan ba zai sa shi bakin ciki ba sai an ce masa watan maulidin Manzo (S.A.W) ya kama.
To ni dai a iya fahimtata tad alibi, in har al’ummar musulmi mun iya daurewa a kan sallar tarawihi ba mu mayar da abin ya zama matsala ba, wadanda suka ga su za su yi ta a jam’i, duk da maganar sayyadina Umar da ya kira da ta bidi’a da kuma wasu bangarorin Musulmi da suka ga za su iya yi a gidajensu, a dakunansu, a daidaikunsu, kuma ba tare da wancan yana zargin wancan ba, shi ma wannan yana zargin wancan ba, kowa yana neman dacewa a wajen Allah, to me zai hana a kan maulidin Manzo (S.A.W) shi ma mu yi hakan? Saboda kai da kake yin sallar asham a jam’I ga hadisi a filii, wanda nan gaba zan kawo wa mai karatu domin ya je ya duba.
Ya dan uwana mai karatu ko da ba a ce maka komai ba, a kan yin jam’i a sallar tarwihi fadinta ko kiranta da sayyadina Umar (R.A) ya yi da bidi’a zai tabbatar maka da  Manzo bai yi ta a jam’I ba. Sayyadina Abubakar (R.A) bai yi ta a jam’i ba, sannan sayyadina Umar (R.A) bai yi ta  a jam’i ba.
Lallai kuwa wannan Magana haka take, saboda da ace Manzon Allah ko sayyadina Abubakar ko sayyadina Umar sun yi, da shi da kansa ba zai kira tad a bidi’a ba, sannan kuma ga wancan hadisin da mai karatu ya karanta a baya wanda Manzo yake cewa: Sallar mutum a dakinsa ita ce ta fi in dai ba sallar wajibi ba.
Tambaya:
1- Ba ka yarda da hadisin da yake cewa Manzon ya yanka abin yanka, aka tambaye shi ya ce saboda murnar ranar haihuwarsa da ta zagayo?
2 – Ba ka yarda da azumin da yake yi ranar Litinin ba, shi ma saboda murnar an haife shi a ranar?
3 – Ka yarda da maganar sayyadina Umar da ya kira sallar tarawihi a jam’I bidi’a ne?
4 – Ka yarda idan sunnar annabi ce ba zai kira tad a bidi’a ba?
5 – Ka yarda sayyadina Umar bai yi ta a jam’i ba?
6 – Ka yarda da sayyadina Abubakar bai yi ta a jam’I ba?
Mai karatu sai ka ba wa kanka amsa, ba ka da bukatar wani ya ba ka amsa, bayan ka ba wa kanka amsa zan sake tambayarka: Don me mai kin maudilin annabi yake kin maulidi duk da ga hujja gamsasshiya? Amma yana kwadaitarwa, ko ma ya fi kowa kwadaitarwa a kan ayi abin da babban sahabin Manzo (S.A.W) Umar dan Khaddabi ya ce bidi’a ne.
Mai karatu sai ka auna da hankali da tunanin da Allah ya yi maka ka ba wa kanka amsa, saboda  ai dukkaninmu mu da muke yin maulidi ko babu komai mun aikata sunnar Manzon Allah, da kuma wanda yake ganin yin maulidi haramun ne kowa yana kaunar Manzon Allah (S.A.W). Sai dai kamar yadda mai karatu ya karanta, soyayyar  Manzon Allah matsayi-matsayi ce.

ABIN MAMAKI (2)
Kai abin mamaki da yawa, masu karantar da  kin maulidi za ka samu su da ake karantarwar suna bin mai karatun ne ba suna bin abin da yake karanta musu ba ne, suna da zukata amma ba sa fahimta, suna da idanuwa amma ba sa gani da su.
To mai karatu, don me ba zan ce da mai irin wannan tunani ba ya fahimtar al’amura da hankalin da Allah ya yi masa, kuma ba ya ganin gaskiya da idanuwan da Allah ya yi masa. Misali: Mai karatu ka dubi asali da dalilin da ya sa ake yin azumin Tasu’a ranar tara ga watan Almuharram na duk shekara, za ka samu hadisin da ya zo da wannan azumi ya ce ne lokacin da Mazon Allah (S.A.W)ya yi hijira daga Makka zuwa Madina, ya tarar da Yahudawan da suke zaune a Madina suna yin azumin rarar tara ga watan Al-muharram. Sai ya tambaye su dalilin yin azumin. Sai suka ce suna yin azumin ne saboda wai ranar aka halakar da Fir’auna, aka kuma tserar da Annabi Musa (A.S) da banu Isra’ila wadanda suka yi imani da shi a wannan lokaci.
Don haka duk shekara suke yin wannan azumi na ranar tara ga watan Al-muharram don godiya ga Allah madaukakin Sarki da ya tserar da su tare da Annabi Musa (A.S) daga Fir’auna. Sai hadisin ya ce: Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Ai ni na fi cancanta  da wannan azumin saboda Musa (A.S)  dan uwana ne.
To mai karatu abin da nake so ka lura da shi a nan shi ne asalin azumin:
1-      Asalin azumin  za ka ga masu yinsa suna gode wa Allah  Ubangijinsu a kan yi musu sha tara ta arziki da ya yi musu, wannan ya sa suka ga ba su iya barin wannan al’amarin ya wuce, sai suka daukar wa kansu yin godiya ta hanyar azumi duk shekara.
2-      Da Manzaon Allah (S.A.W)ya tambaye su, hadisin bai ce sun ce da Manzo (S.A.W) sun kasance suna yin wannan azumin  tare da Annabi Musa (A.S) ba,  kuma ba su ce Annabi Musa (A.S) shi ne ya umare su da su yi azumin ba,  kuma ba su ce da Manzo (S.A.W) iyayensu da kakanninsu da suka wuce su suka ce musu Annabi Musa (A.S) ya umarce su da yin wannan azumin ranar tara ga Muharram ba.
3-      Idan zan tambaye ka kai mai karatu, na ce da kai: Da Annabi Muhmmadu (S.A.W) da kuma Annabi Musa (A.S) wane ne gaba da wani? Ga Ubangiji Allah? Na san za ka ce mini Annabi Muhammadu (S.A.W).
4-      Tsakanin al’ummar Annabi Muhammadu (S.A.W)da ta Annabi Musa (A.S) wacce ce Allah ya fifita? Na san za ka ce al’ummar Annabi Muhammadu (S.A.W).
Wanda fadin Allah a cikin Alkur’ani mai girma da yake cewa: ‘Kun kasance mafificiyar al’umma da aka fitar daga cikin mutane, kuna umarni da kyakkyawan aiki kuma kuna hani a mumunan aiki, kuma kuna yin imani da Allah.’
“KUNTUM KHAIRA UMMATIN UKHRIJAT LINNASI TA’AMURUNA BIL MA’ARUFI WA TANHAUNA ANIL MUNKARI WA TU’UMINUNA BILLAHI”.
(كنتم خير أمة أخرجت للنا س تامرون بالمعروف وتنهون عن المنكر وتؤمنون بالله).[17]
To idan kuwa haka ne, haka abin yake, mai karatu ko da ban ce da shi komai ba, na san zai iya ba wa kansa amsa ta hanyar dan bayanin  da na yi, da kuma ayar da na kawo masa. Idan har  al’ummar  Annaabi Musa (A.S) ba su  manta da sha tara na arziki da Allah ya yi musu, wannan ya kai su da kirkirar azumi saboda su gode wa Ubangijinsu a kan waccar ni’imar da ya yi musu (tserar da su daga Fir’auna), duk da tsawon lokacin da aka dauka in ka dubi tun daga Annabi Musa (A.S) har zuwa lokacin Manzon Allah (S.A.W) amma ba su manta ba.
Wannan yana nuna wa mai karatu kenan har lokacin Annabi Isa (A.S) suna yi, kuma bai hana su ba, har ya zo lokacin Annabi Muhammad (S.A.W), wanda yake shi ne Annabin karshe, kuma shari’arsa ta shafe dukkanin shari’o’in da suka gabata, amma shi ma da ya zo bai ce kun kirkiri bidi’a ba!
Maimakon ya hana su, sai ma ya kara  kamar yadda hadisin ya zo ya ce: Ai Annabi Musa (A.S) dan uwana ne, don haka ni ne na fi cancanta da na yi azumi saboda shi, maimakon ya hana su sai ya tabbatar da shi, saboda soyayyarsa ga Annabi Musa (A.S). To ashe in da za mu kalli wannan hadisin da idanuwan basira za mu ga ya zama dole in har za mu amsa sunan mafificiyar al’umma, dole sai an sami aiki ba wai da baki kawai ba.
Idan har banu Isra’ila (Yahudawa) za su tuna da wancan tagomashi da Allah ya yi musu, har su rinka yin azumi, to ina ga mu da  Allah ya yi mu cikin al’ummar Manzon Allah(S.A.W),? Mu ne muka fi cancanta da mu yi godiya ga  Allah fiye da mutanen Annabi Musa (A.S).
Mai karatu a matsayinka na mai imani kuma mai hankali, don me  za ka haramta wa kanka abin da Allah da Manzonsa suka halasta maka ba su haramta maka ba?!
Ai ko da a ce ban taba jin hadisin da Manzon Allah (S.A.W) ya yi yanka ba, kuma har aka tambaye shi dalilin yankan, ya ce saboda murnar zagayowar ranar haihuwarsa ne. kuma ban taba jin hadisin da Manzon Allah (S.A.W) aka tambaye shi dalilin da ya sa yake yin azumin litinin ba, ya ba da amsa da cewa: Saboda a ranar aka haife shi godiya yake yi ga Allah (S.W.T), to wannan hadisin ya ishe mu mu yi maulidin Annabi domin nuna godiyarmu ga Allah.
Mai yiwuwa mai karatu ya ce: ‘To ai su Yahudawan da Annabi ya samu suna azumi ko Annabi musa  ya yi ne. Sai na ce ka duba hadisin da kyau. Bai ce Manzon Allah Musa (A.S) ne ya ce su yi ba.
Hadisin yana nuna sun ga ya dace da su gode wa Allah ta wannan hanyar (ta azumi). To ashe ka ga idan ka koma baya kamar yadda ka karanta a ma’aunin shari’a shi ne, abin da Manzo (S.A.W)ya zo muku da shi ku karbe shi ku aikata shi, abin da kuma ya hane ku ku bar shi ka da ku aikata shi. Sai ka kara fahimtar gaskiya.
Misali da na kawo maka na dan Taimiyya ya yarda da maulidin Annabi, har ma yake cewa duk wanda ya yi ba don koyi da Nasara ba to zai sami ladan  yin hakan saboda soyayyarsa da Manzon Allah (S.A.W).
Idan har za ka ce: Ya Allah ina kamun kafa da aiki kaza da na yi, kuma Allah ya biya maka to ina ga Manzon Allah (S.A.W) wanda aka yi duniya da lahira dominsa, duk da yake ransu yana yin baki su ji an ce Allah ya yi wani abu domin Manzo (S.A.W)?!

RAGE SON ANNABI
Ka dauki aikin Hajji, in dai ka je kabarin Manzo (S.A.W) kana yin addu’a to za su ce maka ai ba ya jinka, don haka ka tafi. Idan kuwa su ka ji kana cewa: Ya Rasulallahi, ko kuma ya Abal Kasim, za su ture ka su ce shirka ne, ransu ya baci idanuwansu su yi ja. Idan kuma aka ce ka biya kudi musamman domin ka ziyarci Manzon Allah (S.A.W) zai ga kawai kai wahalalle ne, kai wasunsu ma suna ganin haramun ne ka tafi kafa da kafa domin ka ziyarci Manzo (S.A.W).
To bari mu ga  wadannan mutane masu son su raba mu da Manzon Allah (S.A.W) ta hanyar rage mana kaunarsa, mu ga sauran malaman musulunci su ma haka suka tafi a kan irin wannan tunanin nasu? A’a, su dai ‘yan tsirarin nan da suke ta dimuwarsu su ne dai suke ta yin baganniyarsu.
Dukkan malaman mazohabobin musulunci sun tafi a kan kwadaitarwa da lada mai yawa ga duk wanda ya ziyarci kabarin Manzo (S.A.W), dogaro da wannan hadisan da suka zo a kan haka, daga cikin hadisan akwai haidisin da Abdullahi dan Umar (r.a) ya ruwaito daga Manzo (S.A.W), ya ce: “Duk wanda ya ziyarce ni bayan wafatina, to hakki ne a kaina na cece shi ranar Alkiyama.” A wani lafazin: Duk wanda ya ziyarce ni ya taso daga inda yake ba don komai ba sai don ziyarata, ya zama hakki a kan Allah ya ba ni cetonsa ranar alkiyama.”
Mai karatu shi fa mai haramta maulidi hatta da ceton da Manzo (S.A.W) zai yi yana da ja, balle ka ce masa bayin Allah na gari da waliyyai  su ma za su yi ceto. Daga cikin malam da suka fitar da wannan hadisin sun hada da:
1)                           Alhafiz Abul Alkasim Addabari, wanda ya  rasu a shekara ta (360), a cikin littafinsa mai suna Mu’ujamul Kabir.
2)                           Alhafiz Abul Hasan Daru Kudni, wanda ya rasu shekara ta (385).
3)                           Hujjatul Islam Abu Hamidul Gazali Asshafi’i, wanda ya rasu shekara ta (505), a cikin littafinsa Ihya’u Ulumiddin, mujalladi na daya shafi na (246).
4)                           Alhafiz Yahya bin Aliyu Alkurshi Al’umawi almaliki, wanda ya rasu shekara ta (662).
5)                           Alhafiz Jalalud Dini Al-Siyudi, wanda ya rasu shekara ta (911), a cikin littafinsa mai suna Jami’ul Kabir, mujalladi na takwas, shafi na (99).
6)                           Alhafiz Abubakar Albaihaki, wanda ya rasu a shekara ta (458), a cikin littafinsa da aka fi sani da Sunanu Baihaki, mujalladi na biyar shafi na (246).
Wannan kadan ke nan daga cikin malaman Musulunci, mutum dari da hamsin da suka ruwaito wannan hadisin na ziyarar kabarin Manzon Allah (S.A.W) da falalarsa.
Allah kada ka karbi rayuwar duk mai son Manzon  Allah (S.A.W) har  sai ka azurta shi da ziyartarsa (S.A.W)
3.  Su ne wadanda idan Allah ya kai ka kabarin Manzon Allah (S.A.W), idan ka tsaya kana addu'a, suka ga zaka dade sai su kore ka, suna ce maka: Shirka ne ka yi addu'a ka yi kamun kafa da Manzon Allah (S.A.W).
Allah ka gafarta wa mahaifiyata da mahaifina da malamaina, Allah ina rokonka domin matsayin Manzo da Ahlu-Baitinsa, Allah ka hada kan musulmi ka saka masu jin dadi da rarrabar musulmi su gane su fahimci rarraba rauni ne, dunkulewarmu shi ne  karfinmu, Allah ka sa  ko da yaushe tunaninmu ya tafi a kan maslahar Musulunci ko da wannan maslahar ta saba da son ranmu, ko za ta sa aljihunmu ya zama ba shi da nauyi, ko za ta sa mu ga kamar mun kasa.
Allah ka sa mu rinka fifita maslahar hadin kan al’ummar Manzon Allah (S.A.W) fiye da maslahar kanmu domin matsayin Manzo (S.A.W).
‘DA DAI SU LOKACIN DA SUKA ZALUNCI KANSU, ZA SU ZO MAKA SUNA MASU NEMAN ALLAH YA GAFARTA MUSU, KUMA MANZON ALLAH YA NEMA MUSU GAFARA, TO DA LALLAI ZA SU SAMI ALLAH MAI KARBAR TUBANSU. KUMA YA YI MUSU RAHAMA".

(( لوأنهم إذ ظلموا أنفسهم جاؤوك فاستغفروا الله واستغفر لهم الرسول لو جدوا الله توابا رحيما))
Kamar yadda wannan ya tabbata a shari'a, Manzon Allah (S.A.W) kafin ya yi wafati da yanzu bayan yayi wafati, mutum ya kan kai kukansa wajen Allah ta hanyar Manzon Allah (S.A.W) kuma Allah ya biya masa bukata.
Duba Ibni Kasar karkashin Tafsirin wannan aya ta zo sama, ya kawo hadisi daga Utibi (r.a) Ya ce: Wata rana ina zaune a kabarin Manzon Allah (S.A.W), sai ga wani Balaraben kauye ya zo kabarin Manzon Allah(S.A.W), Inda Balaraben kauye ya zo wajen kabarin Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Ya Rasulallahi, na ji Allah ya ce: Ya jawo wannan ayar da ta gabata Ya ce: Lallai ni na zalunci kaina, na zo wajenka domin ka roka mini gafara a wajen Allah.
Sai ya karanta wadannan baitocin:

ياخير من دفنت بالقاع أعظمه
فطاب من طيبهن القاع و الاكم
نفسي الفداء لقبر أنت ساكنه
فيه العفاف وفيه الجود والكرم
Ma'ana:
“Ya mafificin wanda aka rufe jikinsa a wannan sararin.
Tuddai da kwarurruka sun yi kamshi da kamshin wannan sararin.
Raina fansa ne da kabarin da kai ne ka ke cikinsa.
A cikinsa akwai kamewa da kyauta da kuma girmamawa.”
Sai ya juya ya tafi. Sai sahabin da ya ruwaito hadisinsa (Utbi) ya ce: Sai barci ya dauke ni. Nan take sai ya yi mafarki da Manzon Allah Ya ce: Wata rana ina zaune a kabarin Manzon Allah (S.A.W), sai ga wani Balaraben kauye ya zo kabarin Manzon Allah (S.A.W), Manzon Allah ya ce: “Ya Utibi ka tafi ka sami wannan Balaraben kauyen, ka fada masa cewa Allah ya gafarta masa.” Tafsirin ibni Kasir.
Kamun  kafa da Manzon Allah Ya ce: Wata rana ina zaune a kabarin Manzon Allah (S.A.W), sai ga wani Balaraben kauye ya zo kabarin Manzon Allah(S.A.W), shi ma sun ce haramun ne tunda ya rasu!
To mai musan kamun kafa da Manzo (S.A.W) to ya zai yi da wannan hadisi na Utibi (R.A).
Na san za ka ce haka ne, an same su ne ta hanyar sahabban Manzon Allah. To kai ka san iya adadin sahabban Manzon Allah? amsar dai dole ta zama a'a.
Babu wani mutum da zai ce ya san iya yawan sahabban Manzon Allah (S.W.A.) gaba daya, babu dadi babu ragi. To idan kuwa al'amarin haka ne, to kai dan uwana menene na tayar da jijiyar wuya a kan masu yin maulidin? Ai ya kamata ka san cewa, sahabban nan da ba ka san iyaka yawansu ba, to kowanne daga cikinsu ya rayu a wurin da ya dace da rayuwarsa bayan wafatin Manzon Allah (S.A.W). Kai tun ma Manzon Allah yana nan, ai sahabbai da yawa sun karbi addini suka koma garuruwansu cikin al'ummarsu domin su isar musu da sako: Wasu kuma suna zuwa su koma ga jama'arsu, har zuwa lokacin da Manzon Allah ya yi wafati.
To ashe ka ga abu ne mai sauki a gare ka ka gane rashin saninka ba ya nufin mayar da wannan abin haram. A'a zai iya yiwuwa wancan sahabin ya ji ga Manzo Allah ko ya yi abu a gabansa bai hana shi ba, kuma ya je ya ci gaba da aiwatar da abin da ya ji ko ya aikata, kuma har ya mutu bai sami wani hani a kan hakan ba, kuma mutanensa sun ginu a kan haka. To me za ka ce da ire-iren wannan misalan?
Shi ke nan rashin saninka da wancan hadisin da wani sahabi ya ji daga Manzon Allah (S.A.W) sai ya zama hujjarka ta haramtawa ko karyata waccan maganar? Ko kuwa kana nufin duk hadisin da babu shi a cikin litattafan hadisan da ka sani wannan ba hadisi ba ne? Ko kuwa bai inganta ba? Ta yadda har idan ka ga wani yana aikata wani abu, idan kai da malamanka ba ku sani ba kuma babu a litattafan da ka sani, shi ke nan wannan ba addini ba ne, duk da ba ka tambayi mai yin aikin ka ji da me ya dogara ba.
Ko kuwa idan ka tambaye shi ka ce da me ya dogara, idan ya ce da hadisin kaza, sai ka ce tun da kai da malaminka ba ku san da wannan hadisin ba sai kawai ku ce da'ifi (mai rauni) ne.
Kai wani lokacin zai iya zama wani aikin da mutum yake aikatawa ma yana da hujja daga Alkur'ani saboda shi mai kokarin haramta maulidi yana kallon abubuwan ne da ido daya, sai ya haramta maka shi kai tsaye, ko kuwa na ce saboda ga shi da idanuwa amma ba ya gani da su, saboda ba shi da tunaninsa na kansa sai abin da aka ce masa. Lokaci guda kuma yana ganin shi yana da 'yancin tunani, saboda yadda ake raya musu a baki, amma a aikace ba haka ba ne.
Misali: Su kira su 'yan bidi'a masu bin Addinin gargajiya da dai sauransu.
Amma fa kada mai karatu ya manta cewa su wadannan mutane masu sukar maulidi su ne masu kiran kansu Ahlus-sunna. Sai na ce da su wace Sunna? Ba dai sunnar Manzo Muhammad dan Abdullahi (S.A.W) ba. Domin shi (S.A.W) babban burinsa shi ne al'umma ta tsira, su kuma sami yardar Allah (S.W.T.).
Don haka ne ya ce: Idan musulmi yana bangon duniya na yamma, wani musulmin yana bagon duniya na gabas, sai wani abu mara dadi na cutuwa ya sami daya daga cikinsu amma dayan bai ji cewa abin ya shafe shi ba, to wannan ba musulmi ba ne.
To ka ga wanda ya zo yake cewa shi ne mai bin sunnar Manzon Allah (S.A.W), amma kullum aikinsa shi ne ya raba kan al'ummar musulmi, al'ummar da Manzo ya sha wahala wajen hada ta, to ka ga ta bayyana wannan yana bin sunnar wani ne ba ta Annabi Muhammadu (S.A.W) ba. Saboda mun ga duk abubuwan da Manzon Allah ya yi horo ga musulmi su yi kusanci a kansu.
Za ka ga irin masu wancan tunanin ba su damu da su ba. Kai ba ma haka ba, suna yakar mai aikata hakan. Misali: ka sami mutum musulmi, ka saka masa suna dan bidi'a ka kuma dauki wani ka ce masa mai yin addinin gargajiya, ka ce da wannan mai zagin sahabbai, ka kuma ware masallacinka daban, ta yadda in da wani musulmi zai je ya yi slla a cikinsa, bayan an kare ya tashi ya fara karanta littafin da musulmi suka  yarda da su, da ya ga wulakancin da bai taba gani ba a rayuwarsa, saboda a wajensu kamar mutum ya yi ridda ne.
Misali bayan an idar da salla, ya tashi ya dauki littafinsa na Dala'ilil Khairati ya ce zai karanta, duk da littafan dala'ilul khairati ba komai ne a cikinsa ba sai tsantsar salatin Manzon Allah (S.A.W), amma fa ba za su kyale ka ka karanta shi ba a cikin masallacinsu. A lokaci guda wai kuma su ne Ahlus-sunna, wanda kuma ba su ba Ahlil-Bidi'a.
Amma fa suma salatin da suke yi ba fa kowa suke yi wa ba face shi (S.A.W), ba sunayen wani suke kira ba sai na Allah da ya yi wa Manzon Allah  (S.A.W).
Ta yaya kai mai bin sunnar dan Taimiyya, sunnar Manzon ta takaita ne kawai ga dangale wando? Wai shin Manzon Allah wane irin wando ya saka da har ya saka shi iya rabin kwarinsa?
Manzon Allah ya saka wando lokacin da ya yi wafati? Wanduna nawa ya bari? Sahabban da ke tare da shi suma sun saka wanduna? Sayyidana Abubakar wando nawa ya bari bayan ya rasu? Umar dan Khaddab wando nawa ya bari bayan da ya koma ga Allah? Kuma iya kwauri ne wadannan da suka bari in har sun bari?
Kamar yadda mai karatu ya gani su  duk abin da zai hada kan al'ummar annabi ba su cika sonsa ba sai sun yi kokari sun kawo wani abin da zai raba kan al'ummar Annabi ya tarwatsa ta. Idan ka kula sosai za ka ga al'ummar Annabi ta hadu, to za ka ji wanda zai fara ware wasu ya ce banda su, shi ne mai kiran kansa Ahlus-Sunna.
Duk wanda ka ji ya tashi yana kira ga abin da Manzon Allah ya umarci musulmi da su yi shi, amma bai saka sharadi ba sai dai sharadin da Manzon Allah ya saka to wannan ba Ahlus-Sunna ba ne a wajen ire-iren wadancan.

MAI KARATU GA TAMBAYA
1. Ga wani ya zo yana wa'azi, a cikin wa'azin nasa yana kira ga musulmi su hadu su zama tsintsiya madauri daya, inda mutum ya shaida da kalmar shahada ita ce babu abin bautawa sai Allah, kuma annabi Muhammadu dan Abdullahi bawansa ne, dan aikensa ne, ya yarda da salla biyar a kullum, kuma yana yi, ya yarda da sauran annabawan Allah da mursalai, wurin da kuke yin aikin Hajji daya ne, watan azumin Ramadananku daya ne, ma'ana kai da shi kuna azumtar watan ramalana, littafin Allah da ya aiko Manzonsa da shi (Alkur'ani) babu bambanci naka da nasa.
Kuma kai da shi kuna kallon Ka'aba idan za ku yi salla, ya ce don haka ko da kun sami sabani da shi a wasu bangarori daban, ko fahimta ta bambanta ku, don haka ya nemi ku zo ku hada kai kamar yadda Manzon Allah ya umarta a wajensa da kuka saba, kowa ya zo da dalilansa a tattauna don a fahimci juna, domin kada ya rinka kallon wani a matsayin yana kan kuskure.
Mu hadu mu yi maulidin annabinmu (S.A.W), mu godewa ni'imar Allah domin mu sami rabauta a ranar gobe. Su wadannan irin wa'azinsu ke nan.
2. Mutum na Biyu:
Shi ne wanda ya ke yiin wa'azi amma fa a cikin wa'azin yana rusa alakar da take tabbatacciya a tsakanin musulmi, ta hanyar kafirta duk wadda ba ya bin ra'ayisa. kullum kokarinsa ya mayar da musulmi kashi-kashi yadda ya so, kuma duk ya tura su wuta. Babu musulmin kirki sai sh, ko da kuwa kana binsa salla, idan kai kana ganin halaccin maulidi to fa kai dan bidi'a ne awurinsa, kowa mai bautar waliyyai da sauransu ne. kuma wani abin mamaki a nan shi ne wai mai irin wadannan aiyukan shi ne Ahlus-sunna.
To mai karatu sai kayi hukunci a nan tsakanin wanda yake bin Manzo a aikace ba wai abaki kawai ba. idan zan tambaye ka cewa, a cikin mutane biyu da na kawo maka waye mai bin sunnar Manzon Allah (S.A.W), mai kokarin karkasa musulmi ko mai kokarin dinke su. Shin dama Manzon Allah yayi umarni da mu rarrabu ne, ko mu karkata wa'azozinmu zuwa ga rarraba? Ko kuma ya umarce mu ne da mu kasance al-umma daya? Na san mai karatu zai ce lallai Manzon Allah ya umarce mu ne da mu dunkule, mu kasance dunkulallu, to dan menene muke ganin sabanin haka a wajen masu kiran kansu ahlis-sunna, wadanda ba su damu da dukkan abin da Manzon Allah ya bari ba, kuma basu damu da su ba, sai wadanda aka dora su akai, ko da kuwa sun karanta ko sun ji ba za su yi amfani da abin da suka karanta ko suka ji ba, sai abin da malaminsu ya ce musu, sabo da gasu da idanu amma ba sa gani da su, gasu da hankali amma ba sa hankalta da shi.

SHUBUHA
Da wadannan dalilai za ka gane masu haramta maulidi ba suna bin sunnar Manzon Allah ba ne, su na bin sunnar dan taimiyya ne, wanda shi hatta ziyartar kabarin Manzon Allah (S.A.W) yana ganinsa amatsayin haramun ne. kai bama ziyartar kabarin Manzo ba, hatta akan ismar Manzon Allah yana da ja!!
Wanda idan Allah ya yarda shi ma zan yi littafi akan maganganunsa da ya yiwa Manzon Allah da ahlin gidansa.
Da masu haramta maulidi su ka ga basu da wata mafita ko sunnar Manzon su haramta maulidi, sai suka koma cikin dimuwar da suka saba, suka koma wajen wanda suke bin sunnarsa (dan taimiyya), suna masu cewa: To ai maulidi ko bikin maulidin annabi da muke yi mu masu maulidi, yana tattare da wasu abubuwa da suke haramun ne a shari'a.
Misali; Suka ce ana hada maza da mata su cakuda a wuri guda wanda yake haramun ne,Sannan ko da bai zama asalinsa bidi'a ba, to ai kebance rana daya a dukkanin garuruwa wannan bidi'a ne.
Mai karatu, idan ba ka manta ba, da ma sun saba saka wa al'ummar Manzon Allah sunaye daban-daban domin su rarraba su. Daga cikin sunayen da suke amfani da su akwai 'yan bidi'a.
Ta nan zan ba wa duk mai irin wannan tunani amsa da cewa: Ko da duk raneku sun zama daidai kafin a haifi Manzon Allah, to mu a wajenmu ranar da aka haifi Manzon Allah ta fi kowace rana daga cikin raneku kamar yadda bayani ya gabata.
Kuma yadda Manzon Allah da kansa ya nuna haka ta hanyar daukar ranar da aka haife shi daga raneku, ya zabi ranar haihuwarsa yake yin azumi. Kuma an tambaye shi ya fadi dalilinsa na yin hakan (wato zaben ranar haihuwar tasa) kamar yadda bayani ya gabata.
Ya ce: yana yin azumin ranar da aka haife shi ne saboda godiya ga Allah, don haka idan ka ga wani na ta kokari a kan ya soki maulidin Manzon Allah (S.A.W) saboda ya rasa hanyar da zai yi sukar abin da musulmi suka dace a kai (maulidin Annabi), sai ya dawo kuma kan ranar da aka zaba ita kadai ita ce ta zama bidi'a, don haka ya zama haramun.
Sai na ce da mai sukar maulidi: Tusa dai ta kure wa bodari, don haka mu a yadda muka fahimci soyayyar Manzon Allah ba ta takaita da fada a baki kawai ba ko kuma a dage wando.
Mai karatu kada ka yi mamaki ga masu sukar maulidin Manzon Allah, saboda kadan ne daga cikinsu suke ganin cewa Manzon Allah ya cancanta a kai masa kuka bayan ya bar duniya kuma ya share maka hawaye, kamar yadda ka karanta zuwa balaraben kauye kabarinsa (S.A.W) in ji su.
Dalili kuwa ba zai rasa samo asali ba daga gabar da wasu suka nuna wa Manzon Allah da 'ya'yan gidansa ba bayan ya yi wafati. E, to haka ne mana, ko ba ka san mai sukar maulidi bai yarda akwai sharifai ba (Jinin Manzon Allah)? Saboda a wurinsa tunda aka yi abin da aka yi a karbala na kashe Sayyidina Husaini jikan Manzon Allah da wadanda ke tare da shi, shi ke nan zuriyar Manzon Allah ta kare.
Sun manta da fadin Allah a cikin Alkur'ani cewa: zuriyar Manzon Allah za ta wanzu, lokacin da aka yi wa Manzo gorin ba shi da da namiji duk sun mutu. Ibrahim Mu'azzam da Alkasim.
Wannan mutumin da ya yi wa Manzon Allah gorin 'ya'ya maza da ya ce ba shi da magaji shi ne As bin Wa'il, wanda Allah ya mayar masa da martani da cewa: Allah ya ba shi alkausara. Daga karshe kuma ya ce: Makiyin Manzon Allah shi ne mai yankakken baya.
Allah ya yi gaskiya, saboda a yau idan ba ire-iren masu kin maulidi ba babu wani mutum a doron kasa da yake jin cewa jinin Manzon Allah sun kare, kuma su ma 'yan kalilan ne, saboda wasau daga cikinsu ba su yarda ba, da a ce zuriyar Manzon Allah (S.A.W) ta yanke. Zuriyar Manzon Allah tana nan, kuma za ta ci gaba da wanzuwa har ranar karshe.
To amma a yau, ina zuriyar As bin Wa'il? Babu ita ta kare. Sai dai za ka iya samun jikokinsa aikace.













IBNI TAIMIYYA DA SON ANNABI
Mai karatu idan ba ka manta ba, na fada maka duk masu haramta maulidi sun dogara ne da maganganun dan Taimiyya da ya yi a kan maulidin Manzon Allah, kuma ba don komai ba, saboda shi dan Taimiyya duk wani abu da ya zo yake nuna daraja ko daukakar Manzon Allah (S.A.W) da 'ya'yan gidansa, to sai ya yi kokarin nuna cewa wannan ruwayar ko hadisin da aka kawo bai inganta ba.
Masu kafa hujja da maganar dan Taimiyya ta rashin ingancin maulidi da ta zo a Munhajussunna, to dan Taimiyya ya rushe wannan magana tasa, da maganar da ya yi daga baya da take nuna ingancin yin maulidi, kamar yadda  ya rubuta   muka gani a littafinsa IKITIDA’U .
Sannan malamai sun yi maganganu a kan wanda ya raya maulidin Manzon Allah (S.A.W), da irin yanayin da muke yinsa.
Mutum na farko shi ne: Malik Al-Uzaffar, wanda ya rasu a shekara ta (630) bayan hijirar Manzon Allah (S.A.W). Ko kuwa wadanda suka fare shi da irin wannan yanayi su ne shugabannin daular Misira wadanda ake kira Fadimiyyun. Ma'ana ana jingina su da Sayyida Fadima (A.S.).
To mai karatu, idan har ka san ko wane ne dan Taimiyya, wadanda suka bunkasa al'amarin maulidi wadanda aka jingina su da Fadima 'yar Manzon Allah (S.A.W), to lallai ya san dan Taimiyya da masu bin 'yan kanzaginsu ba za su taba yarda da abin da aka jingina shi zuwa ga Manzon Allah da iyalan gidansa ba.
Ba za su goyi bayan wannan abin ba, sai dai in sun ga babu yadda za su yi, saboda duk wanda ya san dan Tamiyya ya san cewa shi mutum ne wanda ba ya boye kiyayyarsa a kan ahlin Manzon (S.W.A.). To ta yaya mai nuna kiyayya da duk wata falala da ya ga ba ta yi daidai da son ransa ba zai yarda da maulidin Manzo (S.A.W).
Mai yuwuwa mai karatu ya yi mamaki, a ce: Ya ya mutumin da ake yi wa lakabi da Shaikhul Islam, amma irin wannan abu ya zo daga gare shi?!
To sai na ce da mai kokwanto, ya duba litattafan da wasu dalibansa suka rubuta a kansa na kura-kuren ibni Taimiyya akan hakkin Manzo da ahalinsa, zia ga abin da bai taba tunani ba, wanda musulmi ba yi musunsu ba, zai ga shi ya musanta su.
Ga masu sukar maulidi na yanzu kuwa, na san cewa da yawa daga cikinsu ba sa son maulidi ne, saboda an ce musu bidi'a ce wacce take haramun, ba wai sun san abin da ya guda na a tarihin musulunci ba. To a yanzu dai in ma sun sani ko ma ba su sani ba, al'amarin dai ya samo asali ne daga abubuwan da suka faru, wanda daidai gwargado tarihi ya rubuta su.
Sannan a cikin litattafan musulmi ga wanda yake bukatar ya sani, ya iya komawa litattafai, wadanda malaman tarihi suka rubuta domin ya san abin da zai iya sani.






HADUWAR MAZA DA MATA A MAULIDI
Masu ganin Maulidi ya haramta saboda wai maza da mata suna haduwa a waje daya, duk mai irin wannan tunani akwai abin mamaki a tare da shi, ko kuwa jahiltar addininsa ya yi, da har zai yi irin wannan tunani. Ko kuwa duk dai neman dalilan da zai yi amfani da su ne wajen haramta maulidin ne, har ya gangaro ga kawo shi ga wannan tunanin. To ya sani a shariar musulunci ana duba asalin abu ne da farko. Shin wannan abin ya halatta?
Akwai dalili daga alkur'ani ko daga ingatattun hadisan Manzon Allah (S.A.W)? Ba kamar irin hadisin da ya gabata ba na fitsari a tsaye, ko kuwa ya sani amma yana kallon abubuwan da ido daya ne, kamar yadda bayani ya gabata.
To asalin dai maulidin Manzon Allah halas ne, don haka tunda jigonsa halas ne, to idan wani abu ya zo daga baya ta bangaren mai aiwatar da shi, sai wannan ya sa duk da halas ne ya koma haram?
Ai in dai jigon abu ya halasta a yi shi, sai a wajen yinsa aka sami wani abu da shari'a ta hana, to a nan shari'a na sanya hukuncin ne a kan wanda ya yi abin, ba wai ka ce gaba daya abin ya haramta ba.
Da a ce dalilin cakuduwar maza da mata zai sa maulidi ya zama haramun, to lallai da abubuwa da yawa sun zama haramun a wannan addinin namu na musulunci. Ga 'yan misalai:
A wajen Musulmi babu wurin da ya fi tsarki kamar Ka'aba, to amma yau ta kai ana yankan aljihun mutane a Ka'aba lokacin da suke dawafi.
Wata kila mai karatu ya ce, to ai aikin Hajji wajibi ne. Tabbas aikin Hajji wajibi ne, to amma ban ce maka aikin Hajji ba, saboda akwai masu zuwa su yi dawafi ba ma a lokacin aikin Hajji ba, saboda yin dawafi a kan kansa ibada ne, kamar yadda kaunar Manzon Allah da 'ya'yan gidansa ta zama ibada.
Kai ita kaunar Manzon Allah da 'ya'yan gidansa wajibi ne ma da fadin Allah, inda ya ke umartar Manzon Allah (S.W.A.): KA FADA MUSU, BA NA TAMBAYARKU LADAN (SHIRYAR DA KU) SAI DAI SOYAYYA GA 'YA'AYN GIDANA.
Idan za mu bi wannan maganar , da sai mu ce duk wanda zai yi dawafi, in dai ba na wajibi ba ne to ya bar shi, saboda a cikin masu yin dawafi akwai mabarnata. Kuma idan mun duba da watan azumin Ramadana ai a goman karshe ana yin sallar tarawihi, kuma maza da mata ne ke zuwa, har ma wasu ba suna fita ne don su yi sallar ba, suna fita ne domin su yi zance ne da 'yan mata, wasu ma ko sallar ba sayi, za ka ga ana yin sallar su kuma suna zance da 'yan mata. Wasu ma har suna zargin masu irin wannan hali mazansu da matansu. Sai ana cikin yin Sallah su kuma su koma gefe suna abin da bai dace ba, ko suke buga wa juna waya (free call).
To ka ga idan haka ne, idan za ka dubi irin wannan wanda har zai sa mai haramta maulidi ya haramta shi saboda yana zargin ana yin wasu abubuwa da ba su dace ba, to da sai ya haramta waccan sallar ta tarawihi, amma ka ga al'amarin ba haka yake ba, duk da ban san mai wannan tunanin shi me ya fahimci cakuda maza da mata a shari'a ba.
Mai karatu in ka duba da kyau, za ka sami abubuwa da yawa da musulunci ya halatta amma a wajen gudanar da su ana samun wasu baragurbi daga cikin mutane da su ba wannan ne yake kai su ba, sai ka ga suna zuwa da abin da yake haramun ne a shari'ance, ba sai a kan taron maulidin Manzon Allah (S.A.W) ba. To don mene ne sai a kan maulidi ne duk da asalinsa halas ne, amma saboda wani abu da shi mai haramtawa yake zargi, shi ke nan sai ya mayar da maulidi haramun, kawai saboda yana zargin wai ana cakuda maza da mata!
Allah ka kara mana kaunar Manzon Allah, ka karbi dan abin da muke iya gabatarwa saboda murnar zagayowar ranar haihuwarsa a wurare daban-daban. A wuraren da muke gabatar da maulidi ayoyin da muke karantawa da hadisan Manzon Allah (S.A.W) da wakokin yabon Manzon Allah da muke rerawa da malamanmu da suke kara mana kaunar Manzon Allah ta hanyar bayanansu, Allah ka amshi wadannan ayyuka namu, Allah ka yarda da mu saboda wanda muke yi dominsa, Allah ka hada kan al'ummar musulmi, ka albarkaci zuriyarmu domin matsayin Manzon Allah (S.A.W).
Allah duk wani mai son raba kan musulmi, ko mai jin dadi da rarraba da musulmi suke ciki ta hanyar kashe-kashen da makiya musulmi ke amfani da su, Allah ka gaji da shi domin matsayin Manzonka (S.W.A.).

ALLAH KA YI TSIRA GA ANNABI MUHAMMAD DA ALAYENSA, KAMAR YADDA KA YI TSIRA GA ANNABI IBRAHIM DA ALAYENSA, DOMIN KAI ABIN YABO NE KUMA ABIN GODEWA.


Husaini Muhammad Kamaye
(Baballe)

GSM: 08037016673
e-mail: baballe7@yahoo.com




[1] Suratul Hadid  (27).
[2] Suratul Ahqaf (9).
[3] Suratul Baqara (117).
[4] Suratun Najmi (3)
[5] Suratu Nun (4).
[6] Suratul Baqara (157).
[7] Suratul Ma’ida (3).
[8] Suratul Ma’idati (114).
[9] Suratul Hashri (7)
[10] Suratu AAli Imran (110)>
[11] SURATUT Tauba (24).
[12]  Suratu AAli imran (31).
[13] Suratun Najmi (31)
[14] Suratun Nahli (125).
[15]  Suratu AAli Imrana (158).
[16] Suratul Hashari (7)
[17] Suratu AAli Imrana (110)

Comments